SLM
Yau nazo muku da yadda ake dafa ganda within some minutes duk taurinta,daga yau Baku basa qusa ko paracetamol ayayin dahuwar ganda.
Dafarko zaki dauki gandarki kisa atukunya kisa ruwa yasha kanta,seki saka kanwa ungurnu babba aciki kirufe,kidora awuta kibarshi yayi tafasa kamar 3.
Zakiga ruwan yayi baqi sosae,seki sauke ki barshi ya huce idan ya huce seki samu soson qarfe ki wanke abarki Tass se bakin yafita da qasar jiki.
Seki sake dorata awuta kisa wata kanwar kadan kibarta taqara tafarfasa,zakiga ruwan yayi danqo seki zubar ki dauraye.
Ki sa kayam qamshi da daddawa da seasoning and spices kisa ruwa kisake dorawa taqarasa dahuwa,wlh daga yau kin dena jiqa ganda tsahon kwana1-2, tasted and trusted.