Kakakin hukumar ‘yansandan Najeriya ya kare sukar da akewa gwamnati kan gurfanar da kananan yara a kotu bisa zargin kifar da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta hanyar zanga-zanga.
A wata hira da gidan Talabijin na Channels TV suka yi dashi, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, basu kai kananan yara kotu ba.
Yace doka tace idan dai yaro ya wuce shekaru 7 za’a iya gurfanar dashi a kotu.
Yace kuma duka cikin yaran mafi karancin shekaru sune wanda ke da shekaru 13.
Yace kuma wadannan yara ne suka rika zanga-zanga ta tayar da hankula da daga tutocin kasashen waje.
Wannan lamari dai ya jawo suka, tofin Allah tsine, da Allah wadai ga gwamnati a ciki da wajen kasarnan.