Kananan yara 32 ne dai gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta gabatar a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatinsa ta hanyar yi masa zanga-zanga.
Yaran dai an gansu cikin dauda da yunwa da rashin lafiya wanda hakan ya jawowa gwamnatin Tinubun Allah wadai.
A wasu bidiyon an ga yaran suna kuka.
Inda a wasu kuma aka gansu suna warwar biskit saboda tsananin yunwa.