Monday, April 6
Shadow

Bayan shan suka daga ciki da wajen Najeriya, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tuhumar cin amanar kasa da akewa kananan yara da aka kai Kotu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tuhumar cin amanar kasa da akewa kananan yara da aka kai kotu na yunkurin kifar da gwamnatin sa ta hanyar zanga-zanga.

Shugaban yace babban lauyan Gwamnati ya duba lamarin dan bayar da shawara kan abinda ya kamata a yiwa yaran.

Yara kanana guda 32 ne dai aka gabatar a babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin cin amanar kasa saboda sun yi zanga-zangar yunwa.

Yaran dai an gansu cikin yunwa da rashin lafiya da firgici inda wasu daga cikinsu suka rika faduwa a farfajiyar kotun.

Tuni dai aka garzaya da guda 5 asibiti.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta ware N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano tace cikin watanni 12 za'a kammalashi

Hakanan an ga bidiyon yanda yaran ke rububin biskit da ruwa da aka basu dan su ci a cikin kotun.

Lamarin ya jawo Allah wadai ga gwamnati a ciki da wajen Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *