Dan majalisar wakilai ta tarayya kuma da a wajan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana cewa ba zai taba biyan kudi a yiwa mutane auren gata a mazabarsa ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yo dashi wadda hutudole ya bibiya.
Yace dalilinsa kuwa baya son ganin karin yawan yara.
Yace a yanzu haka a Arewa yawanmu ya wuce kima amma kuma bamu da isashshen ilimi.
Lamarin yawa da almajirci na kananan yara dai a bayyane yake a Arewacin Najeriya.