Bayanai daga babban bankin Najeriya sun nuna cewa yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu a watanni 3 na biyu na shekarar 2024.
Man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu da kaso 4.51% cikin 100 inda a yanzu Najeriya ke hako ganga Miliyan 1.27 a duk rana.
A watanni 3 na farkon shekarar 2024 kuwa, Najeriya na hako ganga miliyan 1.33 ne wanda hakan ke nuna cewa an samu koma baya kenan.
An dora alhakin hakan akan satar danyen man da kuma lalata bututun man fetur din wasu bata gari ke yi a yankin Naija Delta.
Hakanan yawan man fetur din da Najeriyar ke hakowa yayi kasa da yawan wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta bukaci kowace kasa ta rika hakowa watau Ganga Miliyan 1.58 a duk rana.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL dai ya sanar da cewa ya kashe Naira Biliyan N62 wajan kula da bututun man fetur din