Jam’iyyar APC me mulki a Najeriya ta gargadi jam’iyyun Adawa da cewa kada su ga jam’iyyar Adawa a kasar Amurka ta kayar da jam’iyya me mulki, A Najeriya hakan ba zai faru ba.
APC ta kara da cewa, Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa a Najeriya a zaben shekarar 2027.
A kasar Amurka dai ‘yar takara jam’iyya me mulki ta Democrat, Kamala Harris ta sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar Adawa ta Republic, Donald Trump wanda shine ya sake zama shugaban kasa a karo na biyu.
Jam’iyyun Labour party dana NNPP sun bayyana hakan da abin nasara wanda suka ce ya kamata hukumar zabe me zaman kanta INEC ta koyi darasi daga zaben.
Saidai a martanin jam’iyya me mulki a Najeriya ta APC ta bakin kakakinta, Bala Ibrahim ta bayyana cewa, hakan ba zai faru ba a Najeriya dan kuwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai sake lashe zabe a shekarar 2027.
Yace duk da gwamnati na daukar tsauraran matakai a yanzu amma nan gaba idan aka fara morar romon wadannan matakan mutanen Najeriya da kansu zasu ce sun Fi son Tinubu ya ci gaba da mulki.