Monday, December 16
Shadow

Abubuwan da Tinubu ya faɗa a taron ƙasashen Musulmi kan yaƙin Gaza

Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa.

Taron wanda aka a fara a yau Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.

Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.

Shugaba Tinubu a bayanin da ya yi a gaban taron ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Gaza, inda ya yi gargaɗin cewa ” an kwashe lokacin mai tsayi ana wannan rikici kuma hakan ya haifar da wahalhalun da ba za su ƙirgu ba.”

Ka zalika ya nuna damuwa kan matsalar kayan agaji a rikicin na Gabas ta Tsakiya.

“A matsayinmu na wakilai daga ƙasashen da suke mutunta adalci da mutuncin ɗan adam da kuma kare rayukan mutane, muna da aikin da ya rataya a kanmu na ganin an dauki matakn dakatar da rikicin cikin gaggawa.

“Bai kamata a ce ana suka ba tare da wani dalili ba. Dole ne duniya ta yi ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Gaza.

Karanta Wannan  A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

“Babu wani burin siyasa ko dabarun soji ko kuma na tsaro da za a fake da su wajen hallaka rayukan mutanen da basu ji ba ba su gani ba,” in ji shi.

Tinubu ya yi kira ga duka ɓangarorin biyu da suke yaƙi da juna da su mutunta dokoki da kuma ‘yancin ɗan adam wanda ya yi daidai da tanade-tanaden dokoki da diflomasiyyar duniya.

Ya ce a “dokokin duniya ƙasashe na da ‘yancin kare kansu, amma kare kan, shi ma yana da iyaka, wanda zai ta fi bisa tsarin diflomasiyya.

Ya ƙara da cewa bai kamata mutanen Gaza rayuwarsu da burikansu da kuma gobensu su zama abubuwan da ake ruguzawa ba a yau.

Tinubu ya nemi a ɗauki matakin samar da ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu wanda hakan zai bai wa kowa ‘yancin gashin kai da gina ƙasarsa da kuma kawo ƙarshen yaƙi.

Karanta Wannan  Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana'ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe

“Ba kawai ra’ayin diflomasiyya ba ne da ya yi daidai da abin da na yi amanna da shi, wannan ra’ayi ne da yake cikin dokokin daidaito da kuma fahimtar juna.

“Domin cimma hakan akwai buƙatar tattaunawa da kuma mutunta tarihi. Duk munsan cewa wannan rikicin ba wai ya fara ba ne a ranar 7 ga watan oktoba na 2023 ba. Amma za a cimma wannan sulhu ne ta hanyar kowa ya sarayar da wani abu da yake jin mallakinsa ne.

“Wannan rikici na da dogon tarihi da matuƙar muni wanda ya haifar da rubuwar kawuna cikin ƙanƙanin lokaci. An riƙa yaɗa hotunan wannan rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa masu ɗaga hankali a wayoyi a faɗin duniya. Don haka akwai buƙatar samar da sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba,” in ji shi.

‘Sasancin cike yake da ƙalubale’

Ya yaba wa Yariman Saudiyya mai jiran gado kan shirya taron, wanda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci kuma zai ba da damar sabunta diflomasiyya da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Ganin Dan Kamfai(pant) a wajan daukar film din Hausa(location) ya jawo cece-kuce

“Hanyar sasancin za ta iya zama cike da ƙalubale, amma za a yi ta cikin tattaunawar gaskiya domin fahimtar juna.

“Amma ƙasashen duniya na da damar kawo sabbin hanyoyin kawar da wannan ƙalubale.” in ji shugaban Najeriyan.

Harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya janyo mutuwar mutum aƙalla 1,200, da kuma yin garkuwa da kusan 251.

Tun bayan nan, Isra’ila ta kaddamar da mamaya kan zirin na Gaza, inda ta kashe sama da mutum 43,000, waɗanda yawancinsu mata ne da kuma ƙananan yara.

Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da farmaki a Gaza har sai ta ga bayan ƙungiyar Hamas da ke iko a Gaza.

Gaza na kuma fuskantar matsananciyar matsalar jinƙai, inda wani rahoto ya yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar “mummunan fari” a arewacin Gaza, kuma yaɗuwar rikicin zai iya jefa rabin al’ummar yankin mutum miliyan 2.3 cikin yunwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *