Shugaban makarantar horas da dalibai ta NTI Professor Garba Maitafsir ya bayyana cewa a cikin daliban karatun digiri na 3, PhD da yake koyarwa akwai wanda bai iya rubuta sunansa ba.
Malamin ya bayyana cewa, a ko da yaushe ya kamata ana duba ingancin ilimin malamai dan samun ilimi a wajan dalibai me kyau.
Ya bayyana hakane a wajan taro karawa juna sani a Kaduna kan aikin lamunta a jihar Kaduna.