Jirgin saman Air Peace yayi saukar gaggawa bayan da yayi karo da tsuntsu.
Jirgin dai zai tashi ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja zuwa Legas inda tsuntsun ya fado masa wanda dole hakan tasa aka fasa tafiyar.
Lauya me rajin kare hakkin bil’adama, Inibehe Effiong dake cikin jirgin yace suna shirin tashine inda jirgin yayi karo da tsuntsun wanda hakan ya jawo iface-iface a cikin jirgin.
Yace an saukesu daga cikin jirgin inda suke jiran a gyarashi ko kuma a canja musu wani jirgin.
Yace abin jin dadi shine jirgin bai kai ga tashi sama ba yayin da hadarin ya faru.