Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta kama tsohon dan majalisar tarayya daga jihar Benue John Dyegh bisa zargin cin hancin Naira Miliyan 18 inda ta gurfanar dashi a kotu.
Dan majalisar wanda ya wakilci mazabar Gboko/Tarka daga jihar Benue ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya dake babban birnin jihar Makurdi ranar Litinin.
Kakakin ICPC, Demola Bakare a sanarwar da ya fitar ranar Talata yace John a ranar May 19, 2014, ya karbi kudi da suka kai N18,970,000.
Yace kudin na aikin gina makaranta ne a karamar hukumar Guma amma aka karkatar dasu zuwa asusun bankin wani kamfani me suna Midag Limited wanda John ke da hannu jari me yawa a ciki.
Hakan ya sabawa dokar aikin gwammati.
Mai Shari’a na kotun,Justice Abubakar ya bukaci a aika da John gidan yarin dake Makurdi har sai ya cika sharuddan belin da aka saka masa na biyan Naira Miliyan 20 da samun mutane 2 da zasu tsaya masa.