Wasu ƴan bindiga haye kan babur sun yi garkuwa da wasu yara maza ɗalibai guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar makarantar sakandire da ke garin Babban Duhu a ƙaramar hukumar Safana da ke jihar Katsina.
Wani malamin makarantar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne da safiyar yau ɗin nan, inda ƴanbindigar suka yi awon gaba da yaran guda huɗu kafin daga bisani yara biyu su tsere.
Malamin ya ƙara da cewa “har kawo yanzu ba bu labarin cewa ƴanbindigar sun kira iyalan yaran domin neman kuɗn fansa.”
Babu wani bayani da ya nuna cewa jami’an tsaro sun bi ƴanbindigar domin ceto yaran guda biyu da suka yi garkuwa da su. Sai dai jami’an tsaro da gwamnati sun sha fadin cewa suna samun nasara a kan ƴanbindigar.