Wednesday, April 15
Shadow

A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa ta yi nasarar yin maganin kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar, George Akume.

Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani Littafi da aka yi kan cika shekara daya da kafuwar Gwamnatin Tinubu.

Yace babu wanda zai yi jayayyar cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi nasarar gamawa da Kungiyar Boko Haram.

Saidai yace har yanzu suna yaki da Kungiyar masu garkuwa da mutane.

Karanta Wannan  An kama yaro dan shekaru 13, da dan shekaru 18 da wani me shekaru 45 da yin Fyade a jihar Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *