Tuesday, February 3
Shadow

Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba, Wayau Tinubun ya mai shiyasa ya samu nasara>>Inji Tsohon Hadiminsa

Tsohon hadimin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari me suna Babafemi Ojudu da yayi aikin bada shawara akan harkar siyasa a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Buhari bai so Osinbajo ko Tinubu su zama shugaban Najeriya ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo na yanar gizo me suna Edmund Obilo’s State Affairs.

Ya kuma ce zagayen neman delegates kadai bai isa ba su ci zabe inda yace kamata yayi ace shugaba Buhari ya baiwa hadimansa baki kan su taimakaw Osinbajo amma yaki.

Yace koda Tinubu ma yawa Buharin wayaune shiyasa ya samu nasara.

Karanta Wannan  Mijina ba Dan iska bane, Sharri kika masa, Matar Sanata Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu inda tace sai ta biya diyyar Naira Biliyan 250 na bata sunan data taiwa mijinta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *