Sunday, December 14
Shadow

Kamfanin BUA yayi magana kan Kammala matatar man fetur din da yake ginawa a Akwa-Ibom

Kamfanin BUA ya yi karin haske kan rahotanni dake yawo suna cewa ya kusa kammala matatar man fetur da yake ginawa a jihar Akwa-Ibom.

Rahotanni sun bayyana cewa, aikin gina matatar ya kai kaso 90 cikin 100.

Saidai a sanarwar da kamfanin ya fitar, yace wannan ikirarin ba gaskiya bane, tabbas yana kan aikinsa na gina mamatar man fetur din wadda zara rika samar da ganga 200,000 duk kullun amma maganar an kai kaso 90 cikin 100 na ginata ba gaskiya bane.

Kamfanin ya kara da cewa, bayan Mamatar man fetur din akwai kuma tashoshin gas na CNG da zai gina.

Karanta Wannan  KALLI HOTUNA YANZU-YANZU: Wani matashi a Bauchi ya hau kan karfen wayar Salula (Mast) ba zai sauko ba sai Dr. Bala Wunti ya yarda zai yi takaran gwamnan Bauchi a 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *