Tuesday, February 3
Shadow

Tsaffin sojoji da suka yi ritaya sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashi

Tsaffin sojoji da suka yi ritaya ranar Talata sun kai kujeru da rumfa a kofar fishin ma’ikatar kudi dake Abuja inda suka yi zaman dirshan suka bukaci a biyasu hakkokinsu.

Dama dai a watan Disamba daya gabata, sojojin sun yi irin wannan zanga-zanga ta neman hakkinsu.

Watanni da yawa sun shude inda ake gayawa tsaffin sojojin cewa, babu kudin da za’a biyasu hakkokin nasu.

Bayan zanga-zangar da suka yi a watan Disamba, an biyasu kaso 50 cikin 100 na hakkokin nasu inda aka musu alkawarin biyan suran amma sunce har yanzu shiru.

Karanta Wannan  Dangote ya nace akan shi fa ba zai mayar da ma'aikata 'yan Najeriya 800 daya kora aiki daga matatar mansa ba saboda bai yadda dasu ba, zasu iya yi masa zagon kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *