Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta bayyana sanda gwammati zata sake yiwa ma’aikata karin albashi.
Ta bayyana hakane ranar Alhamis a ziyarar da ta kai jihar Abia.
Tace a baya sai bayan shekaru 5 ne ake karawa ma’aikata Albashi amma a yanzu, za’a rika yin karin albashinne duk bayan shekaru 3.
Tace nan da kasa da shekaru 2 za’a sake yiwa ma’aikatan karin Albashi.