Sunday, January 12
Shadow

Gobarar California: Masu kashe gobara sun yi kadan, an fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka

Masu kashe mahaukaciyar gobarar garin Los Angeles na jihar California a kasar Amurka sun yi kadan duk da yawansu ya kai dubu bakwai da dari biyar.

Lamarin yayi kamari ta yanda saida aka fito da masu laifi da ake tsare dasu a gidan yari dan su taimaka.

A rahoton NPR, tace masu laifi sama da 900 ne aka fito dasu daga gidan yari dan su taimaka a kashe gobarar da taki ci ta ki cinyewa.

Hakanan rahotanni sun tabbatar da cewa, kasar Mexico dake makotaka da kasar ta Amurka ma ta aika da ma’aikatan kashe Gobara dan su taimaka a kashe mahaukaciyar gobarar.

A baya dai, hutudole ya kawo muku cewa ana tsaka da fama da wannan gobara kuma sai ga girgizar kasa a jihar ta California.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Za mu kubutar da dukkanin ƴan Najeriyar da ke hannun masu gârkụwą da mutane, inji shugaban ƴansanda na ƙasa IGP Egbetokun

Sama da mutane 5000 ne suka shaida cewa sun ji motsin kasa San Francisco bay dake da nisan mil 350 da garin Los Angeles inda gobarar ke ci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *