Friday, December 5
Shadow

Gobarar California: Masu kashe gobara sun yi kadan, an fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka

Masu kashe mahaukaciyar gobarar garin Los Angeles na jihar California a kasar Amurka sun yi kadan duk da yawansu ya kai dubu bakwai da dari biyar.

Lamarin yayi kamari ta yanda saida aka fito da masu laifi da ake tsare dasu a gidan yari dan su taimaka.

A rahoton NPR, tace masu laifi sama da 900 ne aka fito dasu daga gidan yari dan su taimaka a kashe gobarar da taki ci ta ki cinyewa.

Hakanan rahotanni sun tabbatar da cewa, kasar Mexico dake makotaka da kasar ta Amurka ma ta aika da ma’aikatan kashe Gobara dan su taimaka a kashe mahaukaciyar gobarar.

A baya dai, hutudole ya kawo muku cewa ana tsaka da fama da wannan gobara kuma sai ga girgizar kasa a jihar ta California.

Karanta Wannan  Da yawa wanda zaka ga sun koma abin tausai a karshen rayuwarsu a lokacin suna tashe sun raina mutane sannan ko ibada basa yi>>Inji Rukayya Dawayya

Sama da mutane 5000 ne suka shaida cewa sun ji motsin kasa San Francisco bay dake da nisan mil 350 da garin Los Angeles inda gobarar ke ci.

1 Comment

Leave a Reply to Gobarar Amerika: Yawan wadanda suka mutu sun karu a yayin da mahaukaciya Gobarar ke ci gaba da yaduwa - Hutudole Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *