Monday, April 6
Shadow

Facebook zai kori ma’aikata dubu uku

Kamfanin Meta dake da mallakar manhajojin Facebook, Thread, Instagram da WhatsApp na shirin korar ma’aikata 3600 daga aiki

Za’a kori ma’aikatan aiki ne saboda rashin kwazo inda za’a maye gurbinsu da wasu kamar yanda kafar Bloomberg ta ruwaito.

Wadannan ma’aikatan na wakiltar kaso 5 na kafatanin ma’aikatan kamfanin na Meta.

Kamfanin dai na da jimullar ma’aikata 72,400.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg ya bayyana cewa ya yanke shawarar mayar da hankali kan kwazon ma’aikata.

Karanta Wannan  Ba akan Dahiru Bauchi aka fara ba, A Tarihin Dariqa babu malaminsu da ya taba cikawa da kalmar Shahada>>Inji Dr. Jameel Matayassara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *