Friday, December 5
Shadow

A karo na 2, Sanata Godswill Akpabio karara ya bayyana tsoron Trump yake ji yayin da ‘yan Najeriya suka bukaci jin Abinda majalisar Dattijai zata ce kan Barhazhanar da Trump din yawa Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa an samu wata sa in sa tsakanin Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau.

A na daf da gama zaman majalisar na ranar Talata ne sai Akpabio yace ‘yan Najeriya da yawa sun mika musu bukatar jin abinda zasu ce kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yawa Najeriya.

Saidai yace wanene shi, bai isa ya baiwa Trump Amsa ba, suna jiran abinda duk Gwamnatin tarayya tace akan lamarin haka za’a yi.

Saidai Sanata Barau Jibrin ya mike yacewa Akpabio ka daina jin tsoron Trump kai ne mutum na 3 mafi mukami a Najeriya kasa me cin gashin Kanta.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kama wasu 'yan Luwadi a Najeriya da abinda aka musu

Barau yace Trump makaryaci ne kuma yawa Najeriya karyar cewa ana yiwa kiristoci kisan kiyashi kuma ya kamata a gaya masa ba gaskiya bane abinda ya fada.

Saidai Akpabio yace shi ba tsoron Trump yake ba, saidai ya bukaci me kula da rubuta abubuwan da aka tattauna a majalisar da ya gaggauta goge kalaman na Sanata Barau Jibrin.

Sannan Akpabio ya kashe lasifikar Sanata Barau Jibrin inda ya hanashi ci gaba da magana.

An ga dai Sanata Barau Jibrin ya tashi ya je kusa da Sanata Godswill Akpabio inda sukai ta musayar kalamai kamin daga baya ya koma kujerarsa ya zauna.

A baya dai, Akpabio ya fito ya karyata wani rahoto da aka ce ya gayawa Trump kalamai marasa dadi inda yace shi bai zagi Trump ba, tsakaninsa da Trump sai girmamawa.

Karanta Wannan  Ji bayanan Bala me rungumar mata, duk da ya tsufa bai tubaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *