
Malamin Addinin Islama, Sheikh Khalifa Sani Zaria ya bayyana cewa, tabbas yawa sojojin dake shirin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki addu’a.
Yace amma ya gargadesu cewa shirin nasu ba zai yi nasara ba dan mutane 2 daga cikinsu zasu ci amanarsu.
An ga wannan jawabi na malam ne a zaman kotun da ake dan ci gaba da sauraren shari’ar wanda ke da hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki.
An tambayeshi amma yasan abinda Jhuyin mulki yake nufi, inda ya amsa yace eh
Da aka tambayi malam me yasa bai kaiwa hukumomi rahoton mutanen ba, sai yace bai san wace hukumace ya kamata ya kaiwa kara ba.
An nadi Bidiyon ne yayin da yake amsa tambayoyin masu bincike kan lamarin inda yace babu wanda ya tursasa masa ya fadi abinda yake fadi, da kansa ne yake wannan bayani