Wani faifan bidiyo da ake ta yaɗa wa ya dauki dai-dai lokacin da John Dramani Mahama ya yi kuskure ya kira shugaban Najeriya, Bola Tinubu a matsayin “Shugaban Ghana” yayin bikin rantsar da shi a yau, 7 ga watan Janairu.
An rantsar da Mahama mai shekaru 65 a matsayin shugaban kasar Ghana a hukumance, inda ya gaji Nana Akufo-Addo.