Friday, December 27
Shadow

A yau Juma’a wata kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya shigar gabanta

Nan gaba a yau, Juma’a ne wata babbar kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya shigar gabanta, inda yake neman kotun ta hana kama shi, sannan kuma a mayar da shi gidan sarki na ƙofar kudu.

Cikin waɗanda sarkin ya shigar da su ƙarar har da ƴansanda da jami’an tsaro na civil defence.

Ranar 28 ga watan Mayu mai shari’a Amobeda Simon ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake ƙarar kada wanda ya hana shi shiga gidan sarki na kofar kudu ko hana shi amfani da duk wasu abubuwan da ya cancanta a matsayin sarki.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: An Bankaɗo Cewa Babu Sa Hannun Alƙalin Da Ake Iƙrarin Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sanusi II

Sannan umarnin kotun ya ce kada fitar da duk wanda yake cikin gidan sarki ba bisa ka’ida ba, har zuwa lokacin da kotun za ta saurari buƙatar da aka gabatar mata.

A yau ne kuma kotun za ta zauna don sauraren ƙorafin da Sarkin, na 15 na Kano ya shigar.

A jiya Alhamis ne wata kotun tarayyar a Kanon da Aminu Babba Ɗan’agundi ya shigar da ƙara gabanta, kan masarautar ta fara zama, inda daga bisani ta ɗage zaman nata zuwa ranar 13 ga watan nan na Yuni, 2024, domin yanke hukunci ko tana da hurumin sauraron shari’ar ko ba ta da shi.

Karanta Wannan  G7 ta amince a yi amfani da kadarorin Rasha da aka ƙwace a ƙasashen duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *