Thursday, October 15
Shadow

A yayin da aka baiwa ‘yan kwallo Najeriya Kyautar Naira Miliyan 150, Tsaffin sojoji sun fito kan tituna suna gangami a biyasu hakkokinsu

Tsaffin sojojin Najeriya sun fito zanga-zanga a yau Litinin dan neman a biyasu hakkokinsh a suke bin Gwamnati.

Taffin sojojin da suka ajiye aiki tsakanin shekarun 2023 zuwa 2024 sun bayyana cewa ba’a musu adalci ba inda suka ce sun shafe shekaru suna aiki amma sun kammala biyan hakkokinsu ya gagara.

Tsaffin sojojin sun gudanar da wannan zanga-zangar ne a ofishin ma’aikatar kudi ta tarayya.

Hakan na zuwane yayin da Gwamnatin tarayya ke rabawa ‘yan kwallo kyautar Miliyoyin Naira da gidaje.

Karanta Wannan  SO GAMON JINI: Murtala Idris Kenan Wanda Tsananin Farin Ciki Da Murnar Auren Mawaƙi Rarara Da A'isha Humaira Ya Sadaukar Da Bijiminsa, Tare Da Alƙawarin Kai Masa Shi Har Garin Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *