Shugaban kasar Kenya, William Ruto yace ba zai iya daukar hayar jirgin sama akan kudi dala Miliyan 150 ba ya dauki tawagarsa zuwa taro a kasar Amurka ba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a kasarsa.
Ya bayyana muhimmancin yin tattalin kudin talakawa inda yace kuma ya kamata shi ya fara nuna alamar abinda yake kira akai, watau rashin almubazzaranci.
A baya dai, shima shugaban kasar Kenyan an zargeshi da yin wadaka da kudin talakawa.