Thursday, May 15
Shadow

Abin da ya sa na ajiye aiki a fadar shugaban ƙasa – Bayani dalla-dalla daga bakin Dr Baba-Ahmed

Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci shugaban ƙasar ya haƙura da neman takarar wa’adin Mulki na biyu a 2027.

Dr Baba-Ahmed wanda ya yi wa shugaba Tinubu aiki a ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya ce ya kamata yayi dattawan da ke riƙe da muƙaman siyasa a yanzu su fahimce cewa lokaci ya yi da za su janye jiki domin bai wa masu jini a jiki damar jan ragama.

Ya shaida wa BBC cewa tsawon lokacin da ya shafe a matsayin mai bayar da shawara ga gwamnatin shugaba Tinubu, ya ga kurakurai da dama da suka bayyana ƙarara cewa gwamnatin ba ta ɗauki hanyar gyara ɓarnar da ta tarar ba. Kuma wannan na cikin dalilansa na ajiye miƙamin sa na bayar da shawara.

Kwanaki kaɗan bayan ya fito ya tabbatar wa duniya cewa ya ajiye miƙamin nasa ne kuma Dr Hakeem Baba-Ahmed ya rubuta wata buɗaɗɗiyar wasiƙa ga shugaba Tinubu, kuma a ciki ya bayyana yadda duk da kasancewarsa a cikin gwamnati amma ya gaza samun damar gabatar da ƙorafi kai tsaye ga shugaban ƙasan.

Karanta Wannan  An gano wata hanyar da 'yan ìndìgà ke amfani da ita dan samun màyàkà da yawa ta hanyar amfani da mata

”Na tafi ne saboda yadda nake ganin alƙiblar gwamnatin, da kuma yadda aka ajiye ni, ni ban ce ba a yi daidai ba, ko na gaya maku ba ji zaku yi ba, ƙasa kuma na ƙara taɓarɓarewa. A waje kuma ana gani na ana cewa ohh, su Dr Hakeem da suna nan da yanzu sun ce kaza.

”Sannan na ce da mun zauna da kai (shugaba Tinubu) da zan ba ka shawara guda ɗaya… idan ka gama wannan shekara huɗu da ƴan Najeriya suka baka, kada ka sake neman shugaban ƙasa. Ka ɗauki wasu matakai na gyara Najeriya ba wai bayan ka ba. Ku nemi ƴaƴanku da jikoki waɗanda a yanzu suna zaune an yi masu takunkumi saboda kwaɗayin irin ku dattawa tsofaffi. Kun ci jiya, kun ci shekaran jiya kuma kuna cin yau.”

Dr Baba-Ahmed ya jaddada cewa idan har shugaba Tinubu ya iya bin wannan shawara to kowacce jam’iyya za ta shiga taitayin ta kuma ta haka ne za a ɗauki hanyar gyara Najeriya.

Karanta Wannan  Kalli Kayataccen hoton Nafisa Abdullahi

Dr Hakeem Baba-Ahmed wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar ayyuka da tsare-tsaren gwamnati kafin ya karɓi muƙamin da ya ajiyen a cikin watan Satumban bara, ya ce akwai banbanci tsakanin jan hankalin gwamnati daga waje da kuma wanda zai yi a cikin gida. ”Ba zai yiwu ka soki gwamnati ba a lokacin da kake mata aiki.”

Tsofaffin hannu da zaɓen 2027

Dangane da shawarar da ya bayar cewa kada shugaba Tinubu ya yi takara a 2027, Dr Hakeem ya yi bayanin cewa dukkan tsofaffin ƴan siyasa ne ya kamata su haƙura da neman mulkin domin bai wa sabon jini dama.

Ya ce ”Ka tara ƴan siyasar da ke neman mulki a yanzu, idan ka samu 100 a cikin su, to za ka samu cewa 80 a ciki daga tsohon gwamna ne ko tsohon minista ko tsohon shugaban ƙasa ko wani tsohon mai neman shugaban ƙasa…waɗanda sun kai da su da ƴaƴansu suke hanƙoron tafiyar da Najeriya. Me kuka yi da, lokacin da kuka tafiyar da Najeriya?”

Karanta Wannan  Sojoji Sun Cafke Katsurgumar Mace, Dillaliyar Alburusai Ga Bello Turji

Ya kuma kore batun cewa matasa ba zasu iya mulkin Najeriya ba saboda tarin matsalolin da ke ƙasa. ”Irin matsalolin da su Sardauna suka samu a Najeriya suna da yawa sosai, amma saboda ƙoƙarin da suka yi wajen warware su ne aka kashe su. ”

Dr Baba-Ahmed ya kuma hasashen cewa ko da shugaba Tinubu ya ƙi karɓar shawararsa kuma ya yi takara a 2027, to ”Yana iya cin zaɓen amma ina ganin kamar samun nasara a wajen shi zai yi wahala.”

A watan Satumban 2023 shugaba Tinubu ya naɗa Dr Hakeem Baba-Ahmed a matsayin mai bashi shawara kan harkokin siyasa, a ofishin mataimakin shugaban ƙasa. Kuma ya wakilci gwamnati a manyan taruka da tattaunawa da dama.

Dama an daɗe ana rade raɗin ajiye muƙamin nasa, amma sai a ranar Asabar 18 ga watan Afirelu ya fito fili ya tabbatarwa duniya cewa ya yi murabus daga aikin nasa, yana mai cewa zai koma gwagwarmayar ceto Arewa da Najeriya daga cikin mawuyacin halin da ta shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *