Wednesday, April 8
Shadow

Alfashar dake faruwa a yankin Arewa ta zarce duk inda ake Tunani, Wai a Arewa ne za’a kama mutum da mata 3 a dakin Otal ya Rhasu>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana takaici kan yanda yanayin lalacewar tarbiyya musamman da yawaitar zinace-zinace suka yi yawa a tsakanin al’umma.

Malam ya bayyana hakane a yayin wa’azin da ya gudanar na Mukhtasar Khalil a masallacin Sultan Bello dake Kaduna Ranar Juma’a.

Malam yace Al’ummar Arewa da aka santa da Kunya da kawaici Yau Tiktok yasa mata sun zama marasa kunya.

Malam yace a Arewa ne aka samu wata mace tace Minista ya mata ciki ya kuma ki daukar nauyin dan.

Yace hakanan a Arewa ne aka samu wani ma’aikacin Kwastam da mata 3 a dakin Otal ya mutu.

Yace dole Allah ya jarrabemu.

Karanta Wannan  Gwamnatin Taryya ta bude shafin baiwa kasuwanci masu rijista bashin Naira Miliyan daya dan kara jari, duba yanda zaku yi rijista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *