
Tauraron fina-finan Hausa, kuma shugaban hukumar fina-finai ta kasa, Ali Nuhu ya kaiwa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya ziyara.
Ali Nuhu yace ziyarar tasa sun tattauna muhimman baututuwa sannan ya samu tarba me kyau.
Ali Nuhu yace daya daga cikin abubuwan da suka tattauna sune naganar gina cibiyar yin fim a jihar Gombe.
Ali Nuhu yace cibiyar zata taimaka wajan karfafa fasaha musamman ta yin fim.
Sannan yace akwai shiri na koyawa daliban jami’ar jihar Gombe yin film.