Saturday, November 8
Shadow

Alummar garin Mokwa na fargabar ɓarkewar cùtùkà saboda gàwàrwàkìn da ba a gano ba

Aƙalla makonni biyu da afkuwar ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane tare da share gidaje masu dimbin yawa a garin Mokwa na jihar Neja, jama’ar yankin na kokawa kan yadda aka soma jin warin gawarwakin mutanen da har kawo yanzu ba a kai ga ganowa ba.

Jama’a dai na ci gaba da bayyana cewa warin na iya haifar da matsala ga lafiya, musamman ana fargabar barkewar kwalara kasancewar da dama daga rijiyoyin jama’a da suke samun ruwan sha sun rufta.

Daga cikin wadanda BBC ta zanta da su, sun ce tun daga ranar asabar ta karshen makon daya gabata suka soma jin warin gawarwakin.

Karanta Wannan  Ya Zama Wajibi Ga Ƴan Nijeriya Mu Tashi Tsaye Wajen Ganin An Kawar Da Gwamnatin APC 2027 A Kowane Matakai, Saboda Mawuyacin Halin Da Ta Jefa Mu, Ta Hanyar Haɗaka Da Muke Shirin Kafawa Nan Gaba Kaɗan, Cewar Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa

Sai dai wasu mazauna garin na Mokwa sun ce a yanzu dai fargabar da ake da ita ta ɗan ragu bayan da aka soma yin feshin magani a wasu wurare.

Sun kuma ce Unicef ta bayar da wasu magunguna da ake sawa cikin ruwan da za ayi amfani da shi masu kashe ƙwayoyin cutuka.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Niger, Dakta Ibrahim Hussaini Audu ya ce tun daga soma samun warin gawarwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu, gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na raba mutane da wurare, da kuma kai musu tsaftattacen ruwa domin sha.

Karanta Wannan  Nan gaba mata ne zasu rika biyan sadaki>>Inji Wannan bazawarar taje mijin aure yaki zuwa dan haka sun koma kasuwanci da hakurin zama da iyaye

Tun bayan aukuwar ambaliyar ruwan ta Mokwa da ta yi matuƙar muni, hukumomi a jihar ta Niger sun ce adadin mutanen da suka mutu sun haura 230, yayin da har yanzu ba gano sama da mutum 400 ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *