Wata amarya a jihar Jigawa ta zubawa abincin walimar bikinta guba.
Dalilin hakan Ango ya kwanta rashin lafiya inda kuma mutum daya daga cikin mahalarta bikin ya mutu.
Lamarin ya farune a karamar Hukumar Jahun dake jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, Shi’isu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan bincike.
Yace sun kama amaryar da wata kuma suna bincike akansu.