A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata.
Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata.
Jami’i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu.
Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000.
Laifin, in ji shi, ya saba wa tanadin sashe na 271 da na 302 na dokar laifuka ta jihar Kaduna.
Lokacin da aka karanta wa wadanda ake tuhumar laifin, Emmanuel ya amsa laifinsa tare da rokon kotu da ta yi masa sassauci yayin da Danbaba ya musanta tuhumar da ake masa.
Lauyan mai gabatar da kara ya roki kotun da ta yi wa Emmanuel shari’a a takaice, sannan ya bukaci a sake sanya wata rana domin gabatar da shaidu don tabbatar da shari’ar da ake yi wa Danbaba.
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun Michael Bawa ya yanke wa Emmanuel hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare Danbaba.
Bawa ya dage sauraron karar har sai ranar 24 ga watan Yuni domin sauraren karar.
Daga: Abbas Yakubu Yaura