Friday, December 5
Shadow

An kama Sojojin da aka sa tsaron makarantar jihar Kebbi amma suka bar makarantar har ta kai ga Tshàgyèràn Dhàjì sun je sun dàukè daliban

Rahotanni daga Abuja na cewa an kama sojojin da aka kai tsaron makarantar MAGA jihar Kebbi amma suka bar makarantar har ta kai ga ‘yan Bindiga suka shiga suka sace dalibai 26.

Daga baya dai dalibai 2 sun tsere daga hannun ‘yan Bindigar wanda hakan ya sa dalibai 24 suka ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan Bindigar.

An kubutar da daliban daga hannun ‘yan Bindigar ba tare da sun cutu ba.

Saidai an yi ta kiraye-kirayen a kama sojojin da aka kao tsaro makarantar.

Wasu sojoji sun shaidawa jaridar Punchng cewa, tuni an kama sojojin da aka kai tsaro makarantar inda ake tuhumarsu kan barin makarantar wanda har ta kai ga ‘yan Bindiga sun shiga sun sace daliban.

Karanta Wannan  Kudin shigar da Najeriya ta samu a shekarar 2023 sunfi yawan kudin da Gwanati tace ta kashe amma duk da haka an ce an ciwo bashi>>Sule Lamido

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *