Monday, June 2
Shadow

An kàshè mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya – NHRC

An kashe mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya – NHRC.

Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, wato NHRC, ta bayyana cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara, an sami aukuwar sace-sacen jama’a kusan 2000, aka kuma halaka wasu kusan 1500 a sassan kasar.

Jami’an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na kuniyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al’amuran kare hakkin bil’adama a kasar, wanda hukumar ta shirya tare da hadin gwiwar ƙungiyar tarayyar Turai, kuma aka gudanar yau a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya ce an sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Satumba na bana.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na shirin soke dokar data halasta auren jinsi na 'yan Luwadi da Magido a kasar Amurka

Hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta Najeriya ta kuma yi tsokaci, cewa an sami ƙaruwar adadin yara ƙanana da ake yi watsi da su a rariya, inda a cikin watan Satumban da ya gabata aka lissafa aukuwar hakan har sau 2723.

Dangane da kisan jama’a da kan auku a Najeriyar kuwa, hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta ƙasar ta danganta hakan da ƙarin ɗibar yara da ta ce ƙungiyoyin ‘yan ta’adda suke yi, kuma suke tafka ta’asa a kasar.

Alkaluman da hukumar kare haƙƙin bil-adaman ta Najeriyar ta gabatar a wajen wancan taro dai sun fayyace ƙamarin munin aukuwar tashe-tashen hankula da keta haƙƙokin bil’adama da ke aukuwa a sassan ƙasar.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan jirgi marar matuki da B0K0 Hàràm suka kaiwa sojoji hari dashi a jihar Borno

Ƙungiyar dai ta bayyana al’amarin da wani abu da ke ci gaba da zama babban ƙalubale, kuma yana nan yana dakon a shawo kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *