Friday, December 5
Shadow

An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa an kayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026.

NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar – don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.

Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.

Karanta Wannan  Kar kowa ya tayar da hankalinsa, Ku bar Trump ya aiko sojojin Amurka Najeriya, Ni kadai gayyane na ishesu>>Inji Mujahid Asari Dokubo

Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Najeriya – inda ya ce ƙoƙari da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *