Ya shaida wa BBC irin ƙalubalen da masu aƙida irin tasa ta rashin yadda da kowane addini ke fuskanta.
Mubarak Bala, shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria kuma fitaccen mai ikirarin rashin addini, ya samu ‘yanci bayan shafe shekaru huɗu a gidan yari kan zargin batanci. An yanke masa hukuncin shekara 24 a kurkuku tun a fari a shekarar 2022, bayan ya amsa laifuka 18 da suka haɗa da batanci, tayar da zaune tsaye, da cin zarafin addini ta kafar sada zumunta.
Hukuncin ya samo asali ne daga wallafa ra’ayoyinsa na sukar addinin Islama, Allah, da Annabi Muhammad (SAW) ta kafar sada zumunta, wanda ya haifar da fushin al’umma. Kafin a yanke masa hukunci, Mubarak ya yi shekara biyu yana jiran shari’a a tsare tun bayan kamashi a Kaduna a ranar 28 ga Afrilu, 2020.
A cewar rahoton BBC, bayan sakin nasa, Mubarak Bala yana zaune a wani boyayyen wuri mai tsaro saboda barazanar rayuwarsa da yake fuskanta. Ya ce, “Duk da samun ‘yanci, har yanzu ina fuskantar barazana ga rayuwata. Wannan damuwa ta tsaro ta kasance lokacin ina tsare kuma har yanzu tana nan.”
Mubarak ya bayyana cewa amincewarsa da tuhumar a shekarar 2022 ta samo asali ne daga kokarinsa na kare kansa da sauran mutane da suka shafi shari’ar. Ya ce, “Na yi imanin abin da na yi wancan lokacin ya ceci rayuwata da wasu mutane a jihar, musamman waɗanda aka haɗa da shari’ar.”
Bayan kwashe shekaru huɗu a tsare, an rage hukuncin ta hanyar kotun daukaka kara wadda ta bayyana hukuncin farko a matsayin mai tsauri. Wannan lamari ya jawo martani daga jama’a da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.