Wednesday, January 15
Shadow

An samu lauyan da zai kare mutumin da ya cinna wa masallaci wuta a Kano

Babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zama a Kano ta ɗage sauraron ƙarar da take yi kan wani matashi da ya cinna wa masallaci wuta a jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu.

A ranar 15 ga watan Mayu ne mutumin da ake zargi a watsa fetur tare da cinna wa masallaci wuta sa’ilin da ake sallar Asuba a ƙaramar hukumar Gezawa ta jiharn Kano.

Ya zuwa yanzu lamarin ya haifar da asarar ran mutum 19, yayin da wasu ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

A lokacin zaman kotun na yau, alƙali ya bayyana cewa an samu lauyan da zai kare wanda ake zargi, inda ya buƙaci a tattara duk wasu bayanai da hujjoji da suka kamata domin miƙa wa lauyan.

Karanta Wannan  Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass, sun yi kira ga Muhammadu Sanusi II yayi koyi da sawun Kakan sa Muhammad Sanusi l da aka cire ya hakura

Kotun ta ɗage shari’ar ne zuwa ranar huɗu ga watan Yulin 2024.

A zaman da kotun ta yi na farko, mutumin ɗan shekara 38 ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a lokacin da kotu ta karanto masa su.

Kimanin mutum 40 ne aka yi ƙiyasin suna cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.

Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Kano ta ce binciken da ta yi na farko-farko sun tabbatar mata cewa wanda ake zargin ya kai hari a masallacin ne sanadiyyar rikici game da rabon gado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *