
Wata kotu a Rwanda ta ɗaure wani malamin addinin Islama har na tsawon shekara biyar a kurkuku sabo da ya kashe wani alade a harabar wani masallaci.
Wasu shaidu uku sun shaida wa kotun cewa sun ga limamin mai suna Sadate Musengimana yana dukan aladen da wani katako matakin da ya kashe shi nan take.
Sai dai lauyansa ya shaida wa kotun cewa ba da gangar ya kashe aladen ba, yana cewa ya yi kokarin koran shi daga harabar wani masallaci da ke gundumar Kayonzo a gabashin kasar ne cikin watan Fabrairu.
“Da yaji yara na cewa wani alade ya shiga masallacin, sai ya fito da wata sanda domin ya kore shi. Ya daki aladen kuma ya mutu, amma bai yi niyyar kashe shi ba,” kamar yadda lauyansa Yusuf Nsengiyumva ya shaida wa BBC.
Lauyan ya ce ya daukaka kara kan wannan hukuncin “mai tsanani”.
Tun watan Fabrairu ake tsare da Liman Musengimana, watan da ya kashe aladen.