Thursday, May 29
Shadow

Ana zargin DPO da yin lalata da karamar yarinya me shekaru 15 da aka tsare a fishin ‘yansanda a Katsina

Ana zargin DPO din ‘yansanda dake Dutsinma, CSP Bello Gusau da yiwa karamar yarinya lalata wadda ake tsare da ita a ofishin ‘yansanda.

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama HRTI ce shigewa yarinyar gaba inda suke nema mata hakkinta.

Shugaban kungiyar Kwamared Maiyasin ya bayyana cewa sai da suka yi bincike suka tabbatar da cewa DPO din ya dauki yarinyar ya je ya kwana da ita a gidansa, ba’a ofishin ‘yansanda ta kwana ba kamin su dauki mataki.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa ya bayyana cewa an dakatar da DPO din inda aka fara bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  Ba su El-Rufai bane ya kamata ace suna yakin nemawa talakawa hakkokinsu ba, saboda mayunwatane da an basu abinda suke so zasu koma gidan jiya>>Sowore

1 Comment

  • Sunusi Adamu Guduma

    Waiyazubillah Allah ka mana tsari da mumunar kadara, Idan ya tabbata gaskiya ne, Ina Amfanin faruwan wannan mumunar aiki? Masu doka a hannunsu kuma sun karya dora, masu kare dukiya da mutuncin Al’umma da rayukan Al’umma kuma ace sune masu karya doka? Allah ya shiryar damu ya gyara mana Al’ummar kasarmu Nigeria.

Leave a Reply to Sunusi Adamu Guduma Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *