Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya dawo daga taron majalisar Dinkin Duniya da ya halarta
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya dawo daga kasar Amurka inda ya halarci taron majalisar Dinkin Duniya.
Kashim ya wakilci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan taron inda ya nemi a baiwa Afrika kujerar Dindindin a majalisar.








