Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Ana zargin Sanata daga Arewa da hannu a matsalar tsàrò, Kalli Bidiyon da aka dauka a gidansa me cike da ban mamaki

Kalli Bidiyo: Ana zargin Sanata daga Arewa da hannu a matsalar tsàrò, Kalli Bidiyon da aka dauka a gidansa me cike da ban mamaki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin wani Sanata daga Arewa da hannu a matsalar tsaro. Sanatan dai daga jihar Bauchi yake sannan Bidiyon ayyukan 'yan Bindiga da aka dauka a wani gida da ake alakantashi da gidan nata yaduwa a kafafen sada zumunta. Da yawa dai sun yi mamaki da ganin hakan. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1963735576302989362?t=XY11jOmB1X9NfhB1Bv2AlA&s=19
A sanya Najeriya cikin addu’o’in Maulidi – Remi Tinubu

A sanya Najeriya cikin addu’o’in Maulidi – Remi Tinubu

Duk Labarai
Mai ɗakin shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta buƙaci al'ummar Musulmi su sanya ƙasar cikin addu'o'in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali. Cikin wata sanarwa da ta fitar albarkacin ranar Maulidin, Remi Tinubu ta aike da saƙon barka ga al'ummar musulmai a faɗin ƙasar. A rana irin ta yau a duk shekara ne miliyoyin Musulmi a faɗin duniya ke bikin domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu (S.A.W). ''Wannan na tuna mana yin koyi da kyayawan halayen Annabi a rayuwarmu ta yau da kullum, ta hanyar nuna soyayya da tausayawa da mutuntawa da haɗin kai'', in ji shi. Ta ƙara da cewa yana da kyau ''mu ci gaba da yi wa ƙasarmu addu'o'in zaman lafiya da ci gaba''.
Najeriya na fuskantar haɗarin faɗawa mulkin kama-karya – Atiku

Najeriya na fuskantar haɗarin faɗawa mulkin kama-karya – Atiku

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce hare-haren da aka kai kan masu gudanar da taro a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi a matsayin abubuwan da ke da haɗarin "jefa Najeriya cikin tsarin kama-karya a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu." A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari tare da tayar da tarzoma a wani wurin taron ƴaƴan jam'iyyar hadaka ta ADC a birnin Kaduna. Cikin mahalarta taron har da jiga-jigan jam'iyyar ta ADC, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma shugaban jam'iyyar na Arewa maso yamma. Daga baya, a jiya Alhamis rundunar ƴansandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta aika da takardar gayyata ga jam'iyyar ta ADC da kuma jagororinta da su bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan hatsaniyar da aka samu a lok...
Mutane miliyan 31 za su faɗa ƙangin yunwa a Najeriya – MDD

Mutane miliyan 31 za su faɗa ƙangin yunwa a Najeriya – MDD

Duk Labarai
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 31 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a Niajeriya, wanda hakan ne mafi yawa a tarihi, sanadiyyar rage kudin tallafi da Amurka da sauran ƙasashen Yamma ke bayarwa. Matsalar yunwar ta fi ƙamari ne a arewa maso gabashin ƙasar inda aka yi ƙiyasin cewa iyalai miliyan 2.3 suka tarwatse a cikin shekara 16 na rikicin Boko Haram. A baya Amurka ce take bayar da kashi 60 cikin ɗari na tallafin jin-ƙai a Najeriya, sai dai shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin. A yanzu ƙasashen Yamma sun mayar da hankali wajen kashe kudi kan tsaro sanadiyyar barazana daga Rasha. A sanadiyyar haka, ala tilas Najeriya ta zabtare kudin da take kasaftawa na tallafin jin-ƙai daga dala miliyan 910 zuwa dala miliyan 300. Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici...
A shekarar da 2023, ‘Yar Arewa, Aisha Abubakar ta shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya sanye da kaya masu dan mutunci, saidai bata ci ba, A shekarar 2025 ta cire kayan mutunci inda ta shiga gasar da kaya masu nuna tsyrayci, saidai a wannan karin ma bata ci ba

A shekarar da 2023, ‘Yar Arewa, Aisha Abubakar ta shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya sanye da kaya masu dan mutunci, saidai bata ci ba, A shekarar 2025 ta cire kayan mutunci inda ta shiga gasar da kaya masu nuna tsyrayci, saidai a wannan karin ma bata ci ba

Duk Labarai
'Yar Arewa, A'isha Abubakar daga jihar Nasarawa, ta shiga gasar cin Sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 2023. Saidai a wancan lokacin A'isha ta rika saka kaya masu alamar mutunci amma bata samu lashe gasar ba. Saidai a shekarar 2025, A'isha ta sake shiga gasar, saidai a wannan karin, ta cire kayan mutuncin inda ta koma saka kaya masu nuna tsiraici. Saidai a wannan karin ma bata ci gasar ba. Da yawa sun rika mata Allah kara. https://www.tiktok.com/@black..melaniin/video/7544467440827141394?_t=ZS-8zTO352OxVJ&_r=1 https://www.tiktok.com/@black..melaniin/video/7544457750613478674?_t=ZS-8zTO6wcB1Jh&_r=1 https://www.tiktok.com/@black..melaniin/video/7544462046876716296?_t=ZS-8zTOI57frDE&_r=1 Ana ci gaba da yada Bidiyon A'isha a kafafen sada zu...
Allah Sarki: Kalli Bidiyon, Cikin Sheshshekar kuka da Shauki, Matashiyar Arewa, Fatima tana bayyana cewa tana son shahararren dan fafutuka na Kudu watau VDM inda tace komai zata iyayi akansa

Allah Sarki: Kalli Bidiyon, Cikin Sheshshekar kuka da Shauki, Matashiyar Arewa, Fatima tana bayyana cewa tana son shahararren dan fafutuka na Kudu watau VDM inda tace komai zata iyayi akansa

Duk Labarai
Matashiya daga Arewa, me suna Fatima ta bayyana cewa, babu wanda take so Duniyarnan sai shahararren dan fafutuka na kudu VDM. Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok inda aka ga ta wallafa Bidiyo tana kuka tana cewa shin wai me yasa mutane suka kasa fahimtarta? A wasu abubuwa data wallafa a shafinta na Tiktok, Hutudole ya hango inda take cewa ita matarsa ce. https://www.tiktok.com/@realteemabfasaha/video/7545212763115752721?_t=ZS-8zT9Gq9Ljcn&_r=1 Da yawa dai na gaya mata cewa hakan ba zai yiyu ba saboda ita musulma ce shi kuma ba musulmi ba. Saidai tace ita idonta ya rufe akan VDM.
Kalli Bidiyo: Anata Rade-radin An yi wani abin kunya a Kano

Kalli Bidiyo: Anata Rade-radin An yi wani abin kunya a Kano

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, wani babba a jihar ya aikata abin kunya. Bidiyo na ta yawo a kafafen sada zumunta a tsakanin Kanawa inda ake alakanta abin kunyar da neman wata karamar yarinya da wani babba yayi. Saidai a cikin duka masu yada wannan maganar babu wanda ya kira suna saidai amfani da wani suna bana wanda ake zargin ba. Bidiyoyin na cewa, wai wanda ake zargin shine ya yi waliccin yarinyar da ga nema saidai a yanzu aurenta ya mutu. Kalli Bidiyon anan https://www.tiktok.com/@hon.danbabangawuna/video/7545932426544008456?_t=ZS-8zTFTj1uH5N&_r=1 https://www.tiktok.com/@dan_sarkeey_kilishi/video/7546215365836082438?_t=ZS-8zTFY8pj1sn&_r=1 https://www.tiktok.com/@dan_abacha2/video/7545606680654974216?_t=ZS-8zTFcT4eOki&_r=1
Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

Duk Labarai
A yayin da Gwamnatin tarayya tace kudin shigarta daga bangarorin da bana danyen ma fetur ba sun karu da kaso 40 cikin 100, tana kuma kokarin kara ciwo Bashi. Gwamnatin dai tace duk da wannan kari data samu na kudin shiga, har yanzu tana fama da karancin kudin gudanar da ayyuka. A baya bayannan, 'yan kwangila sun gudanar da zanga-zanga inda suke neman a biyansu kudin ayyukan da suka yi a shekarar 2024 da suka kai Naira Tiriliyan 4. Domin cike gibin wannan karancin kudin, Gwamnatin tarayya na shirin ciwo bashin Dala Biliyan $1.75bn dan gudanar da ayyuka. Saidai hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa sun samu duka kudin shigar da suke bukata dan gudanar da ayyuka a shekarar 2025, ba zasu kara ciwo bashi ba a wannan shekarar.