
Watanni 7 bayan da Kotun koli tace a rika baiwa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannun gwamnoni ba har yanzu ba’a aiwatar da hukuncin ba
Watanni 7 kenan tun bayan da kotun koli ta yi hukunci inda tace a daina baiwa gwamnoni kudaden kananan hukumomi inda tace a rika baiwa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye.
Saidai har yanzu gwamnatin tarayya bata fara aiwatar da wannan hukunci ba, wanda wasu masana na ganin hakan kin girmama bangaren shari'a ne ganin cewa kotun koli itace kotu mafi girma a kasarnan.
Dama dai tun a wancan lokaci, Gwamnoni sun shigar kara inda suka nemi dakatar da hukuncin amma basu yi nasara ba.
A ranar July 11, 2024 ne kotun kolin karkashin jagorancin me shari'a Lateef Fagbemi SAN ta yi wannan hukunci.
Gwamnatin tarayya a kokarin kawo tsaiko wajan aiwatar da wannan hukunci ta baiwa gwamnatocin jihohi watanni 3 su gudanar da zabukan kananan hukumomi dan fara aiwatar da wannan doka amma shiru ka...