Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Wani sabon bala’i Breziya dubu bakwai, Kwanan nan zaku rika ganin ‘yan mata babu breziya>>Inji Nafisa Ishak

Kalli Bidiyo: Wani sabon bala’i Breziya dubu bakwai, Kwanan nan zaku rika ganin ‘yan mata babu breziya>>Inji Nafisa Ishak

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Nafisa Ishak ta koka da cewa sabon kalubalen da suke fuskanta shine wai Breziya ta kai dubu bakwai. Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok inda tace 'yan mata su rika amfani da leda. Tace kwanannan za'a fara ganin 'yan mata babu rigar nono: https://www.tiktok.com/@nafisa_ishak/video/7543269637975248146?_t=ZS-8zErVYbNeFs&_r=1
Kalli Bidiyon: Ashe tun a watan Yuni an yi Bidiyo aka nuna cewa an sace karafan titin jirgin kadan Abuja zuwa Kaduna amma ba’a dauki mataki ba, jirgin ya ci gaba da jigila

Kalli Bidiyon: Ashe tun a watan Yuni an yi Bidiyo aka nuna cewa an sace karafan titin jirgin kadan Abuja zuwa Kaduna amma ba’a dauki mataki ba, jirgin ya ci gaba da jigila

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana dake nuna cewa, a watan Yuni an bayyana yanda aka sace karafan dake rike da titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna amma ba'a dauki mataki ba. A jiya ne dai jirgin kasan yayi hadari inda mutane 6 suka jikkata sannan wani mutum daya ya rasu kamar yanda rahoton ya nunar. A Bidiyon an ga yanda wani ke nuna karafan jirgin kasan a kwance babu wani karfe dake rike dasu. https://twitter.com/SasDantata/status/1960709922456240269?t=1GmcdDRXOxRusyElFRE9HQ&s=19
Yau Jihar Jigawa Take Murnar Cika Shekaru 34 Da Kirƙirar Ta, Inda Ayyukan Tsohon Gwamna Sule Lamido Suka Karaɗe Kafofin Sada Zumunta Musamman A Tsakanin ‘Yan Jihar

Yau Jihar Jigawa Take Murnar Cika Shekaru 34 Da Kirƙirar Ta, Inda Ayyukan Tsohon Gwamna Sule Lamido Suka Karaɗe Kafofin Sada Zumunta Musamman A Tsakanin ‘Yan Jihar

Duk Labarai
Yau Jihar Jigawa Take Murnar Cika Shekaru 34 Da Kirƙirar Ta, Inda Ayyukan Tsohon Gwamna Sule Lamido Suka Karaɗe Kafofin Sada Zumunta Musamman A Tsakanin 'Yan Jihar Ko kuma kuna da Gwamnan da kuka fi tunawa da shi a jiharku a lokacin irin wannan ranaku? Daga Abubakar Shehu Dokoki
Nasan Gyare-Gyaren da nake sun jefa ‘yan Najeriya a wahala amma nan gaba za’a ga alfanunsu, Ku dauka kamar maganine me daci, idan za’a sha ba dadi amma ana samun waraka>>Shugaba Tinubu

Nasan Gyare-Gyaren da nake sun jefa ‘yan Najeriya a wahala amma nan gaba za’a ga alfanunsu, Ku dauka kamar maganine me daci, idan za’a sha ba dadi amma ana samun waraka>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan Gyare-Gyaren tayar da komadar tattalin arziki da yake yi sun jefa 'yan Najeriya a rayuwar wahala. Yace amma maganar gaskiya gyaran ya zama dole kuma nan gaba za'a ga amfaninsa. Shugaban ya bayyana hakane a yayin ganawar da yayi da 'yan Najeriya mazauna kasar Brazil inda ya nemi hadin kansu wajan ciyar da Najeriya gaba. Ya kuma nemi a hada kai dan zaman lafiya da kawo ci gaba ga Najeriya.
Bidiyo: Kaso 80 na matsalar Najeriya Gwamnoni ne saidai su yi ta rawar Omologo basa gayawa shugaba Tinubu gaskiya>>Inji Farfesa Usman Yusuf

Bidiyo: Kaso 80 na matsalar Najeriya Gwamnoni ne saidai su yi ta rawar Omologo basa gayawa shugaba Tinubu gaskiya>>Inji Farfesa Usman Yusuf

Duk Labarai
Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa, Kaso 80 na matsalar Najeriya gwamnoni ne. Yace Gwamnonin basa gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaskiya. Yace shugaba Tinibu yace ya basu kudin tallafi a saukakawa mutane rayuwa amma babu abinda suke yi. Yace akwai yunwa a Najeriya inda yayi kira ga shugaban kasar yayi wani abu. Farfesa ya bayyana hakane a wata hira da Trust TV ta yi dashi. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1960341287711719707?t=rU-5mlNrWyWoqRkTOwYbTw&s=19
Kalli Bidiyon yanda Babban dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda ake sace man fetur a Najeriya fiye da wanda Najeriyar take samu

Kalli Bidiyon yanda Babban dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda ake sace man fetur a Najeriya fiye da wanda Najeriyar take samu

Duk Labarai
Dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda yace Turawa ke satar danyen man fetur daga Najeriya fiye da wanda Gwamnatin Najeriyar ke samu. Yace ya je inda ake hako man fetur amma aka hanashi karasawa ainahin inda ake fitar da man. Yace shugaban wajan ya kawo masa makudan kudade yace ya karba ya hakura da maganar zuwa ya gani dan kuwa idan yace sai ya je ya gani za'a iya kasheshi. Yace baturen dake aiki a wajan ya gaya masa cewa ko turawa nawa za'a kashe sai an sake kawo wasu saboda irin man fetur din da suke samu ta barauniyar hanya ya kai kusan ganga Miliyan 5 a yayin da Gwamnati kuma ke samun ganga Miliyan 2. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1960465128756851014?t=jRQzQrw4Rr2PfNmTvTutxA&s=19
Kotu ta kwace Naira Miliyan 246 daga hannun tsohon soja, Major-General U.M. Mohammed (Retd.)

Kotu ta kwace Naira Miliyan 246 daga hannun tsohon soja, Major-General U.M. Mohammed (Retd.)

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Lagos ta kwace hannun jari da darajarsa ta kai Naira Miliyan 246 daga hannun tsohon soja wanda ya rike hukumar kula da kadarorin hukumar sojojin Najeriya, NAPL watau Major-General U.M. Mohammed (Retd.). Mai shari'a, Justice Chukwujekwu Aneke ne ya bayyana hakan inda yace a wallafa maganar a gidajen jaridu inda yace kwace kadarorin na wucin gadi ne dan haka suna kiran duk wanda yake da hujjar da zata hana a kwace kadarorin dindindin yayi magana. A sabuwar shari'ar da aka yi wadda mai shari'a, Justice Dehinde Dipeolu yayi hukunci, yace a yanzu an kwace hannun jarin dindindin daga hannun tsohon sojan.
Kalli Bidiyo: Ina da Karama, Kuma ina gaya muku ko dai a taso a taimaka mana wajan kokarin kawo zaman lafiya da muke a Arewa ko kuma abinda za’a gani nan gaba sai yafi abinda ake ciki yanzu>>Inji Sheikh Musa Asadussunnah

Malamin Addinin Islama, Sheikh Musa Asadussunnah ya gargadi yankin Arewa da cewa a taso a goya masa baya ka yunkurin da yake na a yi sulhu da 'yan Bindiga. Malam yace zaman lafiya suke neman a kawo. Ya kuma kara da cewa, amma idan ba'a zo aka goya musu baya ba, nan gaba bala'in da za'a gani yafi wanda ake cikinsa. https://www.tiktok.com/@hassanahmadtsakuwa/video/7543030471500860678?_t=ZS-8zDnV2lUKNk&_r=1