Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Duk Labarai
Tsohon Dakta Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam'iyyar APC. Tsohon Sanatan ya bayyana cewa watsi da waɗanda suka taimaki shugaba Tinubu na daga dalilin da yasa ya fice daga jam'iyyar. Wane fata zaku yi masa? https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1961314229559951402?t=a6UUyHaZzHPEwDWCm_jwkg&s=19
Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Duk Labarai
Me kamfanin sayar da motar Manga Motors ya sha Alwashin baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira 500,000. Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa Abdullahi kyautar Naira 200,000 wanda hakan ya jawo cece-kuce. Da yawa dai na ganin kudin da Gwamnatin tarayya ta baiwa Nafisa sun yi kadan matuka musamman lura da cewa kwanannan aka baiwa 'yan kwallo mata kyautar dala $100,000 kowannensu.
Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai ba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba

Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai ba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton dake cewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a shekarar 2027. Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin dan uwansa, Azibaola Robert inda yace Jonathan bai ce zai tsaya takarar shugaban kasa ba ko ba zai tsaya ba. Hakan na zuwane yayin da PDP ke cewa tana son tsayar da ko dai Goodluck Jonathan ko Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027. Rahotanni sun ce tuni Goodluck Jonathan ya fara tuntubar manyan mutane a kasarnan kan tsayawa takarar shugaban kasar.
Matatar man fetur ta Dangote tasa matatun man kasashen Turai dole suna kullewa saboda kasashen Afrika sun daina sayen man su, na Dangote suke saye

Matatar man fetur ta Dangote tasa matatun man kasashen Turai dole suna kullewa saboda kasashen Afrika sun daina sayen man su, na Dangote suke saye

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, matatun man fetur na kasashen Turai sun fara kullewa saboda kafuwar matatar man Dangote da kuma yanda kasashen Afrika suka koma sayen man fetur a hannun matatar man ta Dangote maimakon sayowa a kasashen turai. Rahoton ya bayyana cewa a baya kamin zuwan matatar Dangote, matatun man kasashen Turai na samar da man fetur ganga miliyan 4.207 amma yanzu saboda zuwan matatar man fetur din Dangote, ganga Miliyan 4.104 suke fitarwa. Hakan ya farune sanadiyyar rufewar matatun man fetur irin su, Grangemouth refiner dake Scotland, da Prax’s da sauransu.

Ji abin mamaki ga rayuwar dan daba daya addabi Kaduna, Watau Habu dan Damusa da aka kashe

Duk Labarai
Habu dan Damusa da ya rigamu gidan gaskiya ya gamu da ajalinsa ne a hannun jami'an tsaro kamar yanda rahotanni suka bayyana. Wasu sun rika murna da mutuwarsa inda wasu kuma suka rika jimami da nema masa rahama. Saidai sabon bayani da ya fito game dashi shine, ashe gadon daba yayi, mahaifinsa ma dan dabane, kuma shima an kasheshi ne ranar da aka haifi Habu Dan Damusa. Hakanan ga habu shima an kasheshi kwana daya bayan da aka haifa masa diyarsa. https://twitter.com/Sarki_sultan/status/1960989309206466569?t=cNfVTM0kI8AqjUnrJ_cgQg&s=19
Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, 'yan Darika sun ji kunya, Sun yi rawa a wajan Maulidi. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da aka ganshi yana wa'azi. Malam ya nanata cewa, Maulidi bashi da Asali a addini. https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7543574023129615622?_t=ZS-8zHMj7MJAuX&_r=1
Karanta Jadawalin kasuwanci guda 17 da Dangote ke yi

Karanta Jadawalin kasuwanci guda 17 da Dangote ke yi

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote na da kasuwanci kala 17. Ga jerinsu kamar haka: Automotive - Kayan MotociCement manufacturing - SimintiEnergy - MakamashiFertilizer - Takin ZamaniLogistics - Kayan amfanin yau da kullu Infrastructure - Raya kasaMaritime - Sufurin TekuMining - Hakar ma'adanaiPetrochemicals - Matatar maiPolysacksReal Estate - Harkar GidajeRefineryRice farming - Noman Shinkafa Salt & seasoning - Gishiri da MagiSugar refining - SukariTomato farming - TimatiriTraining academy - Makaranta.
Na ji dadin Dawowa Najeriya, Kuma ina gina sabuwar Najeriya fil>>Shugaba Tinubu

Na ji dadin Dawowa Najeriya, Kuma ina gina sabuwar Najeriya fil>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya ji dadin dawowa Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen Japan da Brazil. Shugaba Tinubu ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace daya daga cikin aikin da 'yan Najeriya suka bashi a shekarar 2023 shine na kulla hadaka da kasashen Duniya dan kawo ci gaba. Shugaban yace a ziyarar da ya kai kasashen Brazil da Japan Najeriya ta kulla yarjejeniya da kasashen a fannonin kudi, sufuri, kimiyya da fasaha da sauransu.
Da Duminsa: Ina cikin tsama mai wuya, ana barazanar rabani da kujerara>>Inji Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari

Da Duminsa: Ina cikin tsama mai wuya, ana barazanar rabani da kujerara>>Inji Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari

Duk Labarai
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya bayyana cewa, Rayuwarsa data sauran ma'aikatan kamfanin na cikin hadari. Yace ana barazanar saukeshi daga kan mukaminsa, inda yace laifinsa kawai shine kyaran da ya kawo a harkar mai a kasarnan kamar yanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi umarni. Ya bayyana hakane a Abuja yayin da kungiyar ma'aikatan man, PENGASSAN ta kai masa ziyara bisa jagorancin shugabanta, Comrade Festus Osifo. Yace suna kokarin ganin an gyara matatun man fetur din Najeriya sun dawo aiki yanda ya kamata.
Matar Gwamnan jihar Borno ta karrama ma’aikataciya me daukar albashin Naira 30,000 data mayar da Naira Miliyan 4.8 da aka tura mata bisa kuskure kyautar Naira miliyan 1

Matar Gwamnan jihar Borno ta karrama ma’aikataciya me daukar albashin Naira 30,000 data mayar da Naira Miliyan 4.8 da aka tura mata bisa kuskure kyautar Naira miliyan 1

Duk Labarai
Matar gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum ta karrama Faiza Abdullahi wadda karamar ma'aikaciyace dake daukar Albashin Naira dubu 30 bayan da ta mayar da Naira Miliyan 4.8 ds aka tura mata bisa kuskure. Hakanan matar gwamnan ta bata kayan abinci da sauran kyautuka. Faiza dake aiki a jami'ar Maiduguri, UNIMAID ta bayyana cewa ta mayar da kudin da aka tura mata ne saboda tsoron Allah.