
Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin ‘yan kasa
Wani lauya me rajin kare hakkin al'umma, Mr. Olukoya Ogungbeje ya kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya take hakkin 'yan kasa.
Ya kai karar Tinubu ne babbar kotun tarayya dake Abuja inda yace Tinubun yana take hakkin 'yan kasa da murkushesu a duk sanda suka yi yunkurin nuna rashin jin dadin mulkinsa ta hanyar zanga-zanga.
Ya kawo musalin Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta na shekarar data gabata inda yace Gwamnatin Tinubu ta murkushe masu zanga-zangar da take hakkinsu na 'yan kasa.
A cikin wadanda yake karar hadda babban lauyan Gwamati kuma Ministan shari'a, Prince Lateef Fagbemi inda yace yana neman kotu ta baiwa majalisar tarayya umarnin fara shirin tsigesu duka daga mukamansu saboda laifukan da suka aikata sun bada damar a tsigesu.
Saidai lauyan Shugaban...