Friday, May 23
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Kalli Yadda Gwamna Zulum Ke Rushe Gidajen Talakawan Jihar Bornon

Kalli Yadda Gwamna Zulum Ke Rushe Gidajen Talakawan Jihar Bornon

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Abunda Gwamna Zulum yake yi wa talakawan jihar sa na rushe gidajen su sam bai dace ba koda kuwa local dillalai ne suka cuce su na saida musu filayen da bana su ba. Na tabbata akwai wadanda da yawa ba su da masaniyar yadda abun yake kuma hakan zai iya zama silar talaucewar mutane da yawa. Ya kamata Gwamnatin jihar ta kama dukkannin dillalan da suka cuci al'umma domin su biya wa 'yanda suka saidawa wurin hakkokinsu, haka zalika Gwamna Zulum shima ya ragewa wa 'yanda hakan ya shafa ...
APC ta kori ministan Buhari, Aregbesola

APC ta kori ministan Buhari, Aregbesola

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida Rauf Aregbesola, a kan zarginsa da yin abubuwan da suka saba wa jam'iyyar. Reshen jam'iyyar na jihar ta Osun shi ne ya tabbatar da korar a wata wasika da ya fitar. Aregbesola, wanda ya kasance ministan cikin gida a lokacin gwamnatin da ta gabata, ya jagoranci wani bangare na jam'iyyar ta APC a jihar, bangaren da aka yi wa lakabi da “The Osun Progressives,” wanda kuma daga baya aka sake masa lakabi da ''Omoluabi Caucus''. Korar tsohon gwamnan ta biyo bayan taron da bangaren da yake jagoranta ne wato Omoluabi Caucus, ya gudanar kuma karkashin jagorancin, Aregbesola. A lokacin taron bangaren ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga APC,inda ya bayar da hujjar raguwar tasirin jam'iyyar a jihar.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya haramta bukukuwan ranar ‘yan Luwadi da Madigo da na tunawa da kkisan da kawa Yahudawa

Shugaban Amurka, Donald Trump ya haramta bukukuwan ranar ‘yan Luwadi da Madigo da na tunawa da kkisan da kawa Yahudawa

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi sabuwar doka data hana hukumar sojoji ta kasar shiga bukukuwan watan ranar 'yan Luwadi da Madigo da ranar Tunawa da kisan da akawa Yahudawa watau Holocaust. Sauran bukukuwan da aka dakatar sun hada dana watan tunawa da tarihin Bakaken fata, dana ranar tunawa da kisan Martin Luther king, da watan tarihin mata da sauransu. Hukumar tsaro ta kasar Pentagon ta bayyana cewa, ta dauki matakan ne dan bin umarnin shugaban kasar na dakatar a tsare-tsaren daidaito na jinsi.
Kalli bidiyon Soja yana kuka da bankwana na karshe kamin a kkasheshi a fagen yaki

Kalli bidiyon Soja yana kuka da bankwana na karshe kamin a kkasheshi a fagen yaki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bidiyon wani sojan kasar Congo ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda aka ganshi yana kuka yana neman a taimakawa iyalansa a basu hakkinshi bayan ya mutu. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=ACuySd7lNTM?si=XjLZLSDaPegjizRY Da alama sojan yana fagen daga ne dan har harbin bindiga da aka masa sai da ya nuna.
Matawalle Ga Amaechi: Jami’an tsaro na sa ido kan ka bisa cewa ƴan Siyasa na yin kisa don samun mulki

Matawalle Ga Amaechi: Jami’an tsaro na sa ido kan ka bisa cewa ƴan Siyasa na yin kisa don samun mulki

Duk Labarai
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi tir da kalaman da tsohon minista kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi kwanan nan. Amaechi ya ce Shugaba Bola Tinubu da sauran ƴan siyasa ba za su mika mulki ga matasa ba tare da an kai ruwa rana ba. A wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a jiya Alhamis, Matawalle ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin “rura wutar rikici.” “Abin takaici ne kuma babbar barazana ga kasa idan tsohon mai rike da mukamin gwamnati zai yi irin wadannan maganganu,” in ji sanarwar. “A daidai lokacin da gwamnati ke aiki tukuru don inganta hadin kan kasa da tsaro, babu wani shugaba mai kishi da zai rura wutar tashin hankali da rikicin siyasa.”

Maganin hawan jini

Hawan Jini
menene hawan jini Hawan jini yana nufin idan jinin dake gudana a cikin jijiyoyinka gudunsa yayi yawa. Idan aka maka gwaji ya nuna 120/80 to baka da hawan jini. Amma indan ya zama 130/80 ko 140/90 ko 180/120 to jininka ya hau. Yawanci hawan jini bai cika nuna wata alama ba. Idan aka barshi ba tare da an nemi magani ba, yana iya kawo ciwon zuciya ko shanyewar rabin jiki. Cin abinci me gina jiki, da cin abinci wanda babu gishiri a cikinsa sosai yana taimakawa wajan magance matsalar hawan jini. Hakanan motsa jiki da shan magani a bisa ka'ida duk suna kawo saukin cutar hawan jini da ikon Allah. Maganin hawan jini ana samunsa ne ta hanyar cin abinci me gina jiki da motsa jiki akai-akai, da shan magani. Idan ana neman maganin hawan jini na gargajiya, muna da maganin hawan ...
WATA SABUWA: Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina

WATA SABUWA: Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina

Duk Labarai
Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina. Ya bayyana hakane bayan da bidiyon ta ya bayyana aka ji tana cewa yanzu basa tare kuma tana musanta cewa an bata kudi da mota. Seaman Abbas ya karyata cewa akwai matsalar kudi data taso tsakaninsu. Kalli Bidiyon nasa anan Bidiyon da Husaina ta yi dai bai yiwa Ordinary President dadi ba inda ya bayyana cewa itama ta yadda da zargin da ake cewa an bashi kudi ya ki bata kenan. Kalli bidiyon hussaina nan A bidiyonsa da yayi magana kan lamarin a wajan shirya shirin da yake yi, ya bayyana cewa, shine ya rika kashe kudi akan case din Husaina amma babu wanda ya bashi ko sisi. Kalli bidiyon anan
An shirya gagarumar zanga-zanga ranar 4 ga watan Fabrairu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

An shirya gagarumar zanga-zanga ranar 4 ga watan Fabrairu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

Duk Labarai
Kungiyoyin fafutuka a Najeriya da suka hada dana Kwadago da sauransu sun bayyana aniyar fara zanga-zanga akan karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100. Sauran kungiyoyin da suka goyi bayan wannan zanga-zangar sun hada da HURIWA,JAF da NASU ta ma'aikatan jami'o'i. Kungiyoyin sun yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga wannan zanga-zangar a yi dasu dan nuna rashin jin dadin karin kudin kiran. Hakanan itama kungiyar SERAP ta bayyanawa hukumar sadarwa, NCC cewa zata kai kara kotu kan lamarin. Saidai NCC din ta yi kira ga kungiyoyin da su zo a yi zaman fahimtar juna dan ta yi bayanin dalilin da yasa aka yi wancan karin.