Sheikh Gumi ya gargadi Shugaba Tinubu inda ya fallasa wani shiri na yunkurin aika malamai Lahira
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya fallasa cewa akwai jami'an leken Asiri na kasar Israel, watau mossad a Najeriya.
Ya kuma yi zargin cewa, akwai yiyuwar kisan Malamai a shigowar Mossad Najeriya.
Malam ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace barin Mossad su samu karfi a Najeriya ba alheri bane.
Sheikh Gumi ya bayar da misali da mutuwar tsohon shugaban kasa, General Sani Abacha inda yace akwai zargi mutuwarsa, domin ya mutu ne jim kadan bayan ganawa da yasir Arafat tsohon shugaban Falasdinawa.
Gumi yace duk wanda ya baiwa shugaban kasar shawarar hada kai da kasar Israela bai bashi shawara me kyau ba.
Ya ce ta yaya ma kasa Irin Israyla me kisan kiyashi za'a bada daa ta shigo Najeriya?








