Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon Tambaya: Rashin Kulawar Mijina yasa na Afkawa Alfasha, Har Ciki ya shiga, menene Mafita?

Kalli Bidiyon Tambaya: Rashin Kulawar Mijina yasa na Afkawa Alfasha, Har Ciki ya shiga, menene Mafita?

Duk Labarai
Wata matar aure ta aikawa da malam Tambayar cewa rashin kulawar da mijinta baya bata tasa ta afka zina . Tace ta gaya masa amma sai yace ta tafi gidansu. Tace bayaj taje gidansu ta yi jini, sai yace ta koma. Tace amma bayan ta koma sai ciki ya shiga kuma ta gano cewa bayan ta yi jinine cikin ya shiga. Tace mijinta yace a zubar da cikin amma ita ta kiya. https://www.tiktok.com/@nuraabunasir/video/7540630374385241351?_t=ZS-8z79hgia69R&_r=1
Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, Jam'iyyar ADC yaudarar talakawa kawai suke ko sun samu mulki babu wani ci gaba da zasu iya kawowa. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Juma'a. Datti na wannan maganar ne duk da cewa, Peter Obi wanda suka yi takara tare a yanzu yana jam'iyyar ADC. Datti dai yace, yana fatan Peter Obi zai koma jam'iyyar Labour party yayi takara acan. Da aka tambayeshi ko zai sake yiwa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa? Datti Baba Ahmad ya ce Eh.
Usman da Umar (AS) zasu iya canja hukuncin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi kuma hakan yayi daidai>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Usman da Umar (AS) zasu iya canja hukuncin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi kuma hakan yayi daidai>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Babba Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, Sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Umar da Usman (AS) zasu iya canja hukuncin sa Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yayi kuma hakan yayi daidai. Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya basu wannan matsayi na cewa, duk hukuncin da suka yi ya zama shari'a. Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yake ranar Juma'a a masallacin Sultan Bello dake Kaduna a ranar 22/8/2025. Wakilin hutudole ya halarci wajan karatun inda malam yayi wannan maganane a yayin da yake bayar da misalin ikirarin 'yan shi'a na cewa, Khalifanci Aliyu (AS) ne ya kamata a baiwa kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya kan hakan. Malam yace ko da ace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya akan hakan am...
Kalli Bidiyo: Yanzu mun gano cewa Tinubu baya kishin Addini, Baya sauraren mu, Muna fatan Allah ya saukeshi karya kara shekara daya akan Mulki>>Inji Malaman da suka tallata Tinubu a 2023

Kalli Bidiyo: Yanzu mun gano cewa Tinubu baya kishin Addini, Baya sauraren mu, Muna fatan Allah ya saukeshi karya kara shekara daya akan Mulki>>Inji Malaman da suka tallata Tinubu a 2023

Duk Labarai
Daya daga cikin malaman da suka tallata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2023 ya fito ya bayyana cewa a yanzu basu tare da shugaban kasar. Yace sun yiwa shugaban kasar kamfe da zuciya daya dan ci gaban Addini, amma sun gano cewa, ba ci gaban addinine a gabansa ba. Yace dan haka suna rokon Allah kamar yanda ya dorashi mulki Allah a saukeshi: https://www.tiktok.com/@yusufautalazio1/video/7539794814984850696?_t=ZS-8z6xC7WQYNc&_r=1
Yayin da Gwamnati ke shirin cire tallafin wutar Lantarki, Kungiyar Kwadago tace hakan zai kara jefa mutane da yawa cikin Talauci

Yayin da Gwamnati ke shirin cire tallafin wutar Lantarki, Kungiyar Kwadago tace hakan zai kara jefa mutane da yawa cikin Talauci

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC tace shirin gwamnati na cire tallafin wutar Lantarki zai jefa dubban 'yan Najeriya cikin wahalar rayuwa, sannan zai durkusar da kasuwanci da yawa da yanzu haka suke fama. Sakataren riko na kungiyar, Comrade Benson Upah ne ya bayyana hakan inda yace cire tallafin, zai karawa rayuwa tsada a Najeriya. A baya dai Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa, Gwamnati zata cire tallafin wutar saboda 'yan Najeriya su rika biyan ainahin kudin wutar da suke sha. Saidai bayan cire tallafin man fetur hakannya jefa mutane da yawa cikin wahalar rayuwa.
Duk me tunanin Tinubu ba zai sake cin zabeba a 2027 mahaukaci ne lamba 1>>Inji Farfesa Haruna Yarima

Duk me tunanin Tinubu ba zai sake cin zabeba a 2027 mahaukaci ne lamba 1>>Inji Farfesa Haruna Yarima

Duk Labarai
Farfesa Haruna Yarima wanda tsohon dan majalisar tarayya ne ya bayyana cewa, duk me tunanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai sake cin zabe a shekarar 2027 ba mahaukaci ne. Yayi fadi hakane a martaninsa ga masu cewa, Tinubu idan bai sauke Kashim Shettima a matsayin mataimaki ba ya dauko wani musamman Kirista ba zai ci zaben 2027 ba. Farfesa Yerima ya bayyana cewa, wannan magana ba gaskiya bane domin kuwa kamin shugaba Tinubu ya dauko Kashim Shettima a matsayin mataimaki, saida ya lura da abubuwa da yawa. Yace dan haka a yanzu ko da wani zai kawo maganar a canja Kashim Shettima a matsayin mataimaki, Shugaba Tinubu ne da kansa zai fara cewa bai yadda ba.
Tinubu ya bar Japan zuwa ƙasar Brazil zai kuma yada zango a Los Angeles – Fadar shugaban ƙasa

Tinubu ya bar Japan zuwa ƙasar Brazil zai kuma yada zango a Los Angeles – Fadar shugaban ƙasa

Duk Labarai
Tinubu ya bar Japan zuwa ƙasar Brazil zai kuma yada zango a Los Angeles - Fadar shugaban ƙasa Fadar shugaban ƙasa ta ce shugaba Bola Tinubu ya zarce Brazil bayan halartar taruka a Japan. A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu zai hada zango a birnin Los Angeles na kasar Amurka kafin ya wuce birnin Brasilia na kasar Brazil domin ziyarar aiki da zai fara daga ranar 24 ga watan Agusta.
Rundunar sojin Najeriya ta ce kiran kare kai ba ya nufin mallakar makami

Rundunar sojin Najeriya ta ce kiran kare kai ba ya nufin mallakar makami

Duk Labarai
Shalkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan kalaman da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi kan batun kare kai daga hare-haren ƴan fashin daji. Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ta fitar ta ce kalaman Janar Musa ba suna ƙarfafa wa mutane mallakar makami ba ne, kamar yadda wasu kafofin labarai a ƙasar ke yaɗawa. ''Abin da yake nufi shi ne ƴan ƙasa su koyi dabarun kare kai da duniya ta amince da su kamar ƙwarewar tuƙi, da judo da ninƙaya da dambe ko kokawa da sauransu'', in ji sanarwar. ''Kalamansa ba sa nufin mallakar makami ta haramtacciyar hanya, saboda yana sane da dokokin Najeriya da suka haramta mallakar makami''. A ranar Alhamis ne cikin wata hira da gidan Talbijin an Channels, Janar Musa ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarun...