Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Tinubu ya naɗa shugaban PenCom

Tinubu ya naɗa shugaban PenCom

Duk Labarai
Tinubu ya naɗa shugaban PenCom Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Opeyemi Agbaje, tsohon Mataimakin Babban Manaja (AGM) na bankin GTBank, a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Fensho ta Ƙasa (PenCom). Agbaje ya taɓa zama Daraktan Gudanarwa a Metropolitan Bank kafin ya bar harkar banki. TheCable ta rawaito cewa wannan naɗin ya zo ne bayan wa’adin kwanaki bakwai da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayar, inda ta nemi a gaggauta sake kafa hukumar gudanarwa ta PenCom, tare da yin gargaɗin shiga yajin aiki idan gwamnati ta ƙi bin umarnin. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, an bayyana shi a matsayin masani mai tasiri a fannoni na kasuwanci, tattalin arziki da manufofin gwamnati. Agbaje ya kammala karatu a Jami’ar Ife (wanda yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo)...
Ku Daina Ɗaukar Abin Da Gwamnoninku Suke Muku Kamar Alfarma Ce, Ko Taimakonku Suke, Haƙƙinku Ne, Cewar Barista Ɗantani

Ku Daina Ɗaukar Abin Da Gwamnoninku Suke Muku Kamar Alfarma Ce, Ko Taimakonku Suke, Haƙƙinku Ne, Cewar Barista Ɗantani

Duk Labarai
Fitattaccen lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Ɗantani, ya ja hankalin al'umma da su daina kallo ko ɗaukan abubuwan da ƴan siyasa ko shugabanni suke musu a matsayin taimako ko wata alfarma domin ba da kuɗinsu suke yin ayyukan ba. Barista Ɗantani wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, ya fara ne da cewa, "Ba fa noma ko wani aiki suka yi aka biya su suke muku aiki da kuɗin ba! Ba Kuɗinsu ba ne! Ba Dukiyarsu Ba ce! Ba Guminsu ba ne! Su da kansu suka fito suka roƙe ku don ku zaɓe su! Suka dinga manna hotunansu (Posters), suna ta ihu suna shiga lungu da saƙo suna barar ƙuri’unku don kawai su riƙe amanar Dukiyarku!". Inji shi. Barista Ɗantani, ya ci gaba da cewa, "Ku sani Haƙƙinku ne, ba fa kuɗinsu ba ne, ba du...
Kasar China na aiki dan samar da Mutum-Mutumi(Robot) da zai rika daukar ciki yana haihuwar jarirai ba gaske irin na na farko a Duniya

Kasar China na aiki dan samar da Mutum-Mutumi(Robot) da zai rika daukar ciki yana haihuwar jarirai ba gaske irin na na farko a Duniya

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar China na cewa, masana kimiyya na kasar na aiki tukuru dan ganin sun samar da Mutum-Mutumi, Robot da zai rika daukar ciki yana haihuwar jariran gaske. Kafar The Telegraph tace kamfanin fasaha na kasar China me suna Kaiwa Technology na kokarin samar da robot din wanda zai zo da mahaifa da zata rika haihuwar jariraan mutane. Nan da shekarar 2026 ne za'a kammala hada robot din wanda farashinsa zai kai Fan £10,000.
Wata Sabuwa: Ana yada rade-radin cewa Rahama Sadau Auren karya ta yi bayan da aka ta kokarin gano wanene mijinta amma abu ya faskara

Wata Sabuwa: Ana yada rade-radin cewa Rahama Sadau Auren karya ta yi bayan da aka ta kokarin gano wanene mijinta amma abu ya faskara

Duk Labarai
Kokarin gano wanene ainahin mijin Rahama Sadau ya faskara inda akai ta yada hotunan mutane daban-daban ana cewa sune suka aureta amma daga baya a gano cewa ba gaskiya bane. Tun bayan daura auren Rahama Sadau da mijinta me suna Ibrahim ake ta kokarin ganin mijin amma abu ya gagara. 'BBCHausa sun ce Rahama Sadau ta tabbatar musu da cewa ta yi aure. Hakanan 'yan uwan Rahama Sadau duk sun tabbatar da cewa ta yi aure. Yawanci ba'a san da maganar auren Rahama Sadau ba sai ranar da aka daura auren. Dan uwan Rahama Sadau, Haruna ya shaida cewa sun yi dabarar cewa kanwar Rahamar, Fati ce zata yi aure dan a kawar da hankalin mutane. Abubuwan da suka sa wasu ke tababar auren Rahamar sune: Ba'a ga mijinta ba. Ba'a san da auren nata ba sai ranar auren. Ba'a yi wani gagarumin ...
Jama’a Ina Neman Taimakon Kudì Domin Duk Mako Uku Sai An Yi Min Allurar Naira Dubu 250, Kuma Sai An Yi Tsawon Watanni Shida Ana Yi Min Allurar, Cewar Malam Nata’ala Na Shìirin Dadin Kowa

Jama’a Ina Neman Taimakon Kudì Domin Duk Mako Uku Sai An Yi Min Allurar Naira Dubu 250, Kuma Sai An Yi Tsawon Watanni Shida Ana Yi Min Allurar, Cewar Malam Nata’ala Na Shìirin Dadin Kowa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Jama'a Ina Neman Taimakon Kudì Domin Duk Mako Uku Sai An Yi Min Allurar Naira Dubu 250, Kuma Sai An Yi Tsawon Watanni Shida Ana Yi Min Allurar, Cewar Malam Nata'ala Na Shìirin Dadin Kowa Fitaccen Jarumin finafinan Hausa, wanda aka fi sani da Malam Nata'ala a cikin shirin Daɗin Kowa yana na neman taimakon jama'a sakamkon yadda jinyar da ya ke fama da ita ta ci kàrfinsa. Cikin wani faifen bidiyo da ya fitar, ya nemi da a taimaka masa domin a duk bayan sati uku sai an yi masa allura...
Yawanci ‘ya’yan fari a Najeriya ‘ya’yan shegu ne, ba ‘ya’yan halas bane>>Inji Binciken Smart DNA Nigeria

Yawanci ‘ya’yan fari a Najeriya ‘ya’yan shegu ne, ba ‘ya’yan halas bane>>Inji Binciken Smart DNA Nigeria

Duk Labarai
Babbar cibiyar binciken kwayoyin halitta na DNA me sunan Smart DNA Nigeria ta bayyana cewa yawan ma'aurata masu neman a musu binciken kwayoyin halitta da 'ya'yansu na karuwa. Cibiyar tace a shekarar 2025 an samu karuwar yin binciken kwayoyin halittar DNA da kaso 13.1 cikin 100. Hakan na kunshene a cikin bayanin da kungiyar ta fitar wanda ya kunshi bayanan data tattara daga watan July 2024 zuwa June 2025. Kafar tace wani abin damuwa shine yawanci musaman 'ya'ya maza na fari da mata ke haifa ba mazajen ne iyayensu ba, daga waje suke shiga da cikin. Rahoton yace kaso 65 na maza 'yan fari 'ya'yan shegu ne a Najeriya yayin da suma mata 'ya'yan fari yawanci ba 'ya'yan halas bane kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito. Saidai rahoton yace yawanci masu yin g...
Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Duk Labarai
Rahoto yace Jimullar kudin da ake baiwa Sanatocin Najeriya 109 a duk wata da suka kai 2.354 sun isa a biya albashin farfesoshi 4,708. Kudin da ake biyan sanatocin ba albashine kadai ba, hadda kudin kula da ofisoshinsu da na kula da mazabunsu. An dade ana mahawara akan albashin 'yan majalisa da malaman makaranta, Musamman Farfesoshi. A kwanannan aka ga Professor Nasir Hassan-Wagini na jami'ar Umaru Musa Yar’adua University, Katsina yana sayar da kayan miya inda yace yana yi ne dan taimakon kansa. Matsakaicin Albashin Farfesa Naira 500,000 ne a yayin da Sanatoci ke karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata. A shekarar data gabata, BBCHausa ta yi hira da Senator Kawu Sumaila wanda yace duk wata Naira Miliyan 21.6 ake biyansu. A hirarsa da Daily Trust, Farfesa Dr Niyi Sunmonu na jam...
Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo

Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo

Duk Labarai
Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo. Ɗan Majalisar Wakilai, mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Fagge, Muhammad Bello Shehu, ya sayi wa injin faci ga wani tsoho da ke buƙatar injin. DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne faifen bidiyon tsohon, mai suna Ali Abdulrahman, wanda aka fi sani da Ali Mai Faransawa, ya karade kafafen sadarwa, inda ya ke korafin cewa ya shafe shekaru ya na tafiyar Kwankwasiyya amma bai taɓa samun wani tagomashi ba. A cewar Ali Mai Faransawa, wani kansila a Fagge ya yi masa alƙawarin haɗa shi da shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge domin a saya masa injin faci, amma abun ya ci tura. Bidiyon ta sa, wacce gidan rediyon Express FM ya wallafa a shafin sa na fa...
Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Zanen Tattoo da Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta yi akan Kirjinta ya jawo cece-kuce sosai. Tun a kwanakin baya aka ga Rahama Kwance ana mata zanen a kirjinta wanda ya jawo cece-kuce sosau. Saidai a yanzu bayan data saki wasu sabbin hotuna, an kuma ganin Tattoo din ya fito sosai fiye da da. Hakan yasa da yawa suka rika tambayar shin me zanen yake nufi dan kuwa da Yarbanci ta rubutashi. Wasu masu fassara dai sun bayyana cewa, zanen na kirjinta na nufin Allah Dukiya.