Monday, May 12
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Shugaban Najeriya, Tinubu ya shiga jerin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3

Shugaban Najeriya, Tinubu ya shiga jerin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3

Duk Labarai
Wani rahoto da ya bayyana, ya nuna shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba Mafi rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3 a Duniya. Wata kungiya me suna, (OCCRP) ce ta bayyana hakan. Ta kuma samu wanna sakamako ne bayan da ta nemi a yi zabe dan fitar da mutane mafiya rashawa a Duniya. Kungiyar ta hada da manyan 'yan Jarida ne da 'yan fafutuka dan kare hakkin al'umma. Shugban kasar Kenya, William Ruto ne ya zo na daya sai kuma shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo ya zo na uku. Hambararren Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ne ya zamo gwarzon shekara.
Ban yi wata murna sosai da zama shugaban kasa ba, saboda irin barnar da na iske n yiwa Najeriya>>Tinubu

Ban yi wata murna sosai da zama shugaban kasa ba, saboda irin barnar da na iske n yiwa Najeriya>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, bai yi wata murna da zama shugaban kasa ba bayan da ya iske irin barnar da aka yiwa Najeriya. A bayyana hakane ga kakakin majalisar dattijai, Godwill Akpabio. Akpabio ne ya bayyana hakan a wajan rabon kayan da yayi ga mutanen mazabarsa wanda suka hada da kayan abinci da ababen hawa da sauransu a jiharsa ta Akwa-Ibom. Yace wata rana ya taba tabayar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan shin ko yayi murnar zama shugaban kasa kuwa lura da irin barnar da ya iske tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele yawa kasar? Sai shugaba Tinubu yace masa murna kadan yayi. Bai san barnar da akawa Najeriya ta kai haka ba. Akpabio ya kara da cewa, ya gayawa shugaban kasar cewa, yayi imanin kamar yanda ya gyara Legas, Itama Na...
Matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne suka fi sayen maganin karfin maza>>Ji Illar da yake a jikin mutum

Matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne suka fi sayen maganin karfin maza>>Ji Illar da yake a jikin mutum

Duk Labarai
Bincike ya nuna cewa, matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne a Najeriya suka fi amfani da maganin karfin maza . Yawanci ana sayen magungunan kara karfin maza ne dan samun kuzari da jin dadin jima'i. Saidai da yawa daga cikin magungunan da ake sayarwa din basu da rijista hukukomin lafiya na kasa basu tantance su ba, hakanan kuma mafi yawan masu sayar da magungunan ma basu da ilimi akan harkar maganin. Hakan yasa ake samun matsalar magungunan su rika bayar da illa ga lafiyar dan adam inda akan samu matsalar mazaje na mutuwa yayin jima'i.
Kada ku yadda da sabuwar dokar haraji>>Sanata Ndume ya gayawa sarakuna

Kada ku yadda da sabuwar dokar haraji>>Sanata Ndume ya gayawa sarakuna

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi kira ga sarakunan dake karkashin mazabarsa da kada su yadda da sabuwar dokar haraji ta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Masarautar Askira, inda yace dalilinsa na kin amincewa da dokar harajin shine wahalar da mutane ke ciki, dan hakane yake kira da sarakunan da suma kada su amince da ita. Yayi kira ga matasa da su tashi su rungumi harkar noma inda yace a daina dogaro da gwamnati da Albashi dan kuwa albashin Naira dubu 70 ba zai sayi buhun shinkafa ba dake Naira dubu 100 ko buhun wake dake Neman kaiwa Naira dubu dari 200. Ya jinjinawa mutanen garin Gwoza saboda jajircewar da suka nuna duk da matsalar tsaron da suke fama da ita inda yace babu yanda za'a yi a rika kawo musu hare-hare ba tare da masu b...
‘Yan Najeriya na cikin wahala a matsin rayuwa, Rabon kayan abinci ba shine magani ba>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Dattijai, Ahmad Lawal

‘Yan Najeriya na cikin wahala a matsin rayuwa, Rabon kayan abinci ba shine magani ba>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Dattijai, Ahmad Lawal

Duk Labarai
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, mutane na cikin matsin rayuwa kuma rabon kayan abinci ba shi bane mafita. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo bayan da ya je mazabarsa dake jihar Yobe ya raba kayan tallafi. Yace kamata yayi a samarwa mutane hanya da zasu dogara da kansu amma rabon abinci zai kawo sauki ne kawai na dan lokaci wanda kuma wahalar zata ci gaba. Saidai yace kamin su kai ga wancan matsayi, su dake da halin bayarwa zasu ci gaba da bada tallafin dan saukakawa mutane rayuwa. Yayi kira ga masu rike da madafan iko dasu dauki matakan da zasu kawowa Al'umma saukin rayuwa.
Muna kyautata zaton farashin man fetur zai sauka>>Inji ‘Yan Kasuwar Man Fetur

Muna kyautata zaton farashin man fetur zai sauka>>Inji ‘Yan Kasuwar Man Fetur

Duk Labarai
Biyo bayan fara dawo da ci gaba da aikin matatar man fetur ta Warri, 'yan kasuwar man fetur sun bayyana kyakykyawan zatom cewa, farashin man fetur din zai sauka. 'Yan kasuwar sun ce yanzu gasa tsakanin masu matatun man fetur na cikin gida zata yi tsanani ta yanda dole za'a sauke farashin man fetur din. Sun bayyana hakane ranar Litinin bayan fara aikin matatar man fetur ta Warri. Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai fara fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan samun kudin shiga. Hakan na zuwane wata daya bayan da matatar man fetur da Fatakwal ta fara aiki.
Bidiyon yanda wata mata ta je kasar Saudiyya tana addu’ar neman miji ya dauki hankula

Bidiyon yanda wata mata ta je kasar Saudiyya tana addu’ar neman miji ya dauki hankula

Duk Labarai
Wani Bidiyo na wata mata data je kasar Saudiyya tana neman mijin aure ya dauki hankula. An ga matar tana rokon Allah ya basu mazaje na gari kuma ya musu maganin matan da basu son mazan su su kara aure. https://twitter.com/abu_twinss/status/1873417995084853639?t=dCJ0iopYxyj4cI2IO7ZqgQ&s=19 Kalli Bidiyon anan A cikin Bidiyon, An jita tana fadar cewa, Allah muna son Aure amma matan sun hana, Allah ka yi mana maganinsu.
Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Duk Labarai
Wani magidanci a kasar Afrika ta kudu ya saki matarsa biyo bayan sumbatarta da mawakin kasar Amurka, Chris Brown yayi. Mutumin me suna Lusaka dan kimanin shekaru 42 ya gamu da takaici ne bayan ganin hotunan sumbatar matarsa da Chris Brown din yayi. Kwanannan dai Chris Brown din ya je kasar Afrika ta kudu inda yayi wasa sannan kuma ya gana da masoyansa inda a canne ya hadu da matar me shekaru 34. Mijin yace abinda matar ta aikata rashin girmamashi ne kuma ya yiwa aurensu bacin da ba zai gyaru ba. Yace kuma abinda matar ta yi bai kamata ace matar aure ta aikata hakan ba. Mijin dai yawa matar magana dan ya mata fada amma sai ta gaya masa cewa, wannan ba wani abin tada hankali bane.